Majalisar Dattawa Ta Naɗa Sabon Jagora da Mataimakin Mai Tsawatarwa
- Majalisar dattawan Najeriya ta maye gurbin David Umahi a kujerar mataimakin shugaban masu rinjaye na majalisa ta 10
- Sanata Godswill Akpabio ya sanar da naɗa Sanata Oyelola Yisa Ashiru daga jihar Kwara a inuwar APC a matsayin wanda zai maye gurbin
- Ya kuma bayyana Sanata Nwebonyi Peter Onyeka a matsayin sabon mataimakin mao ladabtarwa na masu rinjaye a majalisar
FCT Abuja - Majalisar dattawa, a zaman ranar Laraba, ta naɗa Sanata Oyelola Yisa Ashiru (APC, Kwara ta Kudu) a matsayin sabon mataimakin shugaban masu rinjaye.
Bayan haka ta naɗa Sanata Nwebonyi Peter Onyeka (APC, Ebonyi ta Arewa) a matsayin mataimakin mai tsawatarwa na majalisar dattawan Najeriya.
Jaridar The Nation ta tattaro cewa shugaban Majalisar Dattawan, Sanata Godswill Akpabio, ne ya sanar da sabbin naɗe-naɗen a zaman mambobi na yau Laraba a Abuja.
Majalisar Dattawa Ta Fara Tantance Sabon Shugaban EFCC da Wasu 2 da Tinubu Ya Naɗa, Bayanai Sun Fito
Sanata Ashiru, wanda kafin wannan naɗi, shi ne mataimakin mai ladabtarwa na masu rinjaye, zai koma sabon mataimakin shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Haka zalika wannan naɗi da aka masa na nufin zai maye gurbin Sanata David Umahi, wanda shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya naɗa shi a matsayin ministan ayyuka.
Umahi, tsohon gwamnan jihar Ebonyi, shi ne mataimakin jagoran majalisar dattawa kafin daga bisani ya yi murabus domin karban mukamin Minista, Daily Trust ta ruwaito.
Majalisa ta amince da naɗin shugaban EFCC
Bayan wannan sanarwa ne, Majalisar dattawa karkashin Sanata Akpabio ta tantance tare da tabbatar da naɗin Mista Ola Olukoyede a matsayin sabon shugaban EFCC.
Ta kuma amince da naɗin Muhammad Hassan Hammajoda a matsayin Sakataren hukumar yaƙi da rashawa EFCC da Halima Shehu a matsayin shugabar NSIPA.
Wannan ya biyo bayan naɗin da shugaban Tinubu ya yi mutanen uku tare da neman sahalewar majalisar a wani saƙo da ya aika ranar Talata, 17 ga watan Oktoba.
Ortom Ya Boye Asusu Sama Da 570, Ya Nuna Guda 25 Kadai, Gwamnatin Benue
A wani rahoton kuma Gwamnatin jihar Benuwai ta bankaɗo badaƙalar yawan asusun bankin da Samuel Ortom ya ɓoye kafin ya bar mulki.
Kwamishinan kuɗi da tsare-tsaren kasafi, Michael Oglegba, ya ce sun gano jihar tana da asusu sama da 600 amma 25 aka nuna wa sabon gwamna.
Asali: Legit.ng