Sanata Ifeanyi Ubah Ya Sauya Sheka Daga Jam'iyyar YPP Zuwa APC

Sanata Ifeanyi Ubah Ya Sauya Sheka Daga Jam'iyyar YPP Zuwa APC

  • Sanata Ifeanyi Ubah ya sauya sheƙa daga jam'iyyar YPP ya koma jam'iyyar APC mai mulki ranar Alhamis, 12 ga watan Oktoba, 2023
  • Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ne ya tabbatar da haka a wasiƙar da ya karanta yayin zamana majalisar
  • A wasiƙar, Sanatan ya bayyana cewa ya ɗauki wannan mataki ne saboda rikicin cikin gidan YPP da ya ƙi ci kuma ya ƙi cinyewa

FCT Abuja - Sanata mai wakiltar mazaɓar Anambra ta kudu a majalisar dattawa, Sanata Ifeanyi Ubah, ya canza sheƙa daga Young Progressives Party (YPP) zuwa APC.

Daily Trust ta tattaro cewa hakan na ƙunshe ne a wata wasiƙa da shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya karanta a zauren majalisar ranar Alhamis.

Sanata Ubah tare da shugaban majalisar dattawa.
Sanata Ifeanyi Ubah Ya Sauya Sheka Daga Jam'iyyar YPP Zuwa APC Hoto: Senator Dr. Patrick Ifeanyi Ubah
Asali: Facebook

Sanata Ubah ya yi bayani a cikin wasiƙar da Akpabio ya karanta cewa ya yanke shawarar barin jam'iyyar YPP ne sakamakon gaza shawo kan rigingimun cikin gida.

Kara karanta wannan

Ombugadu Na PDP Ya Yi Martani Kan Batun Cewa Zai Tube Rawanin Sarakuna Da Zarar Ya Hau Mulki a Nasarawa

Sai dai Sanatan bai bayyana ainihin rikicin cikin gidan da yake nufi ba, wanda a cewarsa, shi ne dailin barin jam'iyyar YPP, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasiƙar ta kara da bayanin cewa Sanata Ubah ya koma APC ne da amincewar mutanen mazabarsa.

Ana ganin wannan sauya sheƙa ta ƙara ɗaga jam'iyyar APC, musamman a irin wannan lokacin da jam'iyyar ke kokarin ganin ta yaɗu a shiyyar Kudu maso Gabas.

Taƙaitaccen tarihin siyasar Sanata Ubah

A shekarar 2014, Ubah ya sha ƙashi a zaben gwamnan jihar Anambara karkashin inuwar jam'iyyar Labour Party.

Haka nan kuma INEC ta ayyana Ubah a matsayin wanda ya lashe zaɓen Sanatan Anambra ta kudu karkashin inuwar jam'iyyar YPP a ranar 24 ga watan Fabrairu, 2019.

A babban zaɓen da ya biyo bayan wannan, wanda aka yi a watan Fabrairu, 2023, Hukumar zaɓe ta sake ayyana Ubah, ɗan shekara 52 a matsayin wanda ya ci zaɓen Anambra ta kudu a karo na biyu.

Kara karanta wannan

Majalisar Wakilai Ta Ƙasa Ta Ɗage Zamanta Yayin da Ɗan Majalisar APC Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

Jigon LP Ya Bayyana Gaskiyar Abinda Ke Cikin Takardun Peter Obi

A wani rahoton kuma Peter Obi ya shiga layi yayin da jigon LP ya fallasa ruɗanin da ke tattare da takardun karatunsa.

Mai magana da yawun LP na ƙasa a tsagin Apapa ya ce sunan Obi ya sha banban a takardar digiri da kuma ta NYSC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262