"Na Yi Amfani Da Sadiq Abubakar Yayin Rubuta WAEC": Atiku Ya Yi Martani Kan Zargin Takardun Bogi
- An zargi Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, a zaben 2023 da kirkirar satifiket na bogi
- Wannan zargin na da alaka ne da satifiket dinsa na kammala makarantar sakandare, wacce ke dauke da wani suna daban da wanda aka sanshi da shi
- Sai dai, Atiku bai musanta ikirarin ba amma ya ce ya yi rantsuwa a kotu na canha sunansa daga Sadiq zuwa Atiku
Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya yi martani kan zargin cewa ya yi jabun takardar shaidar jarrabawar kammala sakandare mai dauke da suna "Sadiq Abubakar".
Atiku, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, a babban zaben 2023, ya tabbatar cewa takardarsa ta kammala sakandare na dauke da sunan "Sadiq Abubakar" amma ya yi rantsuwa na kotu ya canja sunansa bayan ya ci jarrabawar.
Dele Momodu, jigo na jam'iyyar PDP, ya tabbatar da martanin na Atiku a wallafar da ya yi a kafar sada zumunta a ranar Talata, 10 ga watan Oktoba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rubutun da ya yi a kafar X ta ce:
"Yan APC masu zumudi suna ta zargin cewa mai gida na Alhaji Atiku Abubakar (GCON) ya kirkiri takardar bogi hakan yasa na tura masa zargin kuma ga amsar da ya bada: "Eh na yi amfani da Sadiq Abubakar yayin rubuta jarrabawar WAEC kuma bayan na ci jarrabawar na yi rantsuwa a kotu na cewa ni ne dai Atiku Abubakar. Na tafi ABU a matsayin Atiku Abubakar kuma ya ci jarrabawa na a matsayin Atiku Abubakar.
"An yi min tambayoyin daukan aiki a Gwamnatin Tarayya a matsayin Atiku Abubakar kuma an dauke ni aiki a Hukumar Kwastam a matsayin Atiku Abubakar. Don haka ina kirkirar ta bogi?" - ATIKU ABUBAKAR."
APC ta magantu kan nasarar da Atiku Abubakar ya samu kan Bola Tinubu a kotun Amurka
A bangare guda, jam'iyyar All Progressives Congress, APC, mai mulki a Najeriya ta bayyana kokarin da Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP ya samu a kotun Amurka na sakin masa takardun Tinubu a matsayin 'ihu bayan hari'.
Duro Mesoko, mataimakin sakataren watsa labarai na jam'iyyar APC ya ce fafutikan da Atiku ya yi na ganin kotu ta amince da bukatarsa 'ihu ne bayan hari."
Meseko ya ce umarnin kotun na Amurka bai damu jam'iyyar APC ba ko kadan, domin Shugaba Tinubu ba domin ba shi da wani abin boyewa.
Asali: Legit.ng