Gwamnoni da Jiga-Jigan PDP Ba Su Halarci Taron da Atiku Ya Gudanar Ba
- Taron manema labaran da Atiku ya gudanar ya ƙara nuna cewa har yanzun wutar rikici na ci gaba da ruruwa a jam'iyyar PDP
- Abun mamakin shi ne babu ko gwamna ɗaya daga cikin gwamnonin PDP 13 masu ci ko yan majalisar da suka halarci wurin
- Hatta abokin takarar Atiku a zaben 2023, Ifeanyi Okowa, da aka yi tsammanin ganinsa a gaba-gaba bai halarta ba
FCT Abuja - Manyan fitattun jam'iyyar PDP na ƙasa ba su halarci taron 'yan jarida na duniya, wanda ɗan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya gudanar a Abuja ba.
Jaridar The Nation ta ce rashin halartar masu ruwa da tsaki a PDP ya ƙara nuna rabuwar kai da rigingimun cikin gida na ci gaba da ruruwa a jam'iyyar.
Babu ko mutum daya daga cikin mambobin kwamitin gudanarwa na PDP (NWC), ciki har da mukaddashin shugaban jam’iyya na kasa, Umar Damagum, da aka hanga a wurin taron, Vanguard ta tattaro.
Haka kuma, babu daya daga cikin gwamnonin jam’iyyar 13 da ke kan karagar mulki ko kuma mambobinta na majalisar tarayya 2 da aka ga ƙeyarsa a wurin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa mambobin NWC ba su halarta ba?
Da yake bayanin maƙasudin rashin zuwansa wurin, kakakin PDP na ƙasa, Mista Debo Ologunagba, ya ce ba ya kusa ne shiyasa bai take wa Atiku baya a taron ba.
Yayin da aka tambayi dalilin da ya sa sauran mambobin NWC ba su halarta ba, Ologunagba wanda ya yi magana ta wayar tarho, ya ce ba shi da ikon yin magana da yawunsu.
Muƙaddashin shugaban PDP na ƙasa, Umar Damagun, bai ɗaga ƙiran da aka masa ta wayar tarho ba, kuma bai turo amsoshin saƙonnin da aka aika masa ba.
Abin mamakin kuma shi ne, babu wani daga cikin mambobin NWC da ya fito aiki ofishinsa a sakatariyar jam’iyyar ta kasa.
Daga cikin wadanda aka yi tsammanin ganinsu wurin taron amma ba su zo ba har da dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Dokta Ifeanyi Okowa.
Wasu jiga-jigan PDP da suka halarci taron sun hada da shugaban PDP na kasa da aka dakatar, Iyorchia Ayu, da tsohon shugaban jam’iyyar, Prince Uche Secondus da sauransu.
"Ban Taba Cin Amanar Shugaba Bola Tinubu Ba" Atiku Ya Maida Martani
A wani rahoton kun ji cewa Atiku Abubakar ya ce bai ci amanar shugaba Bola Tinubu ba a lokacin da suka haɗa ƙawancen siyasa a zaɓen 2007.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya yi iƙirarin cewa maimakon haka ya yi wa Tinubu halacci a shekarar 2003.
Asali: Legit.ng