"Ban Taba Cin Amanar Shugaba Bola Tinubu Ba" Atiku Ya Maida Martani

"Ban Taba Cin Amanar Shugaba Bola Tinubu Ba" Atiku Ya Maida Martani

  • Atiku Abubakar ya ce bai ci amanar shugaba Bola Tinubu ba a lokacin da suka haɗa ƙawancen siyasa a zaɓen 2007
  • Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya yi iƙirarin cewa maimakon haka ya yi wa Tinubu halacci a shekarar 2003
  • A cewarsa tun lokacin da tsohon gwamnan Legas ya nemi zama abokin takararsa a 2007 suka raba gari a siyasance

FCT Abuja - Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya yi iƙirarin cewa bai taɓa cin amanar shugaban ƙasa Bola Tinubu ba a lokacin da suka ƙulla ƙawance a 2007.

Atiku ya ce a maimakon cin amanar Tinubu, ya tsaya tsayin daga a tsakaninsa da shugaban ƙasa na wancan lokacin, Cif Olusegun Obasanjo, domin kar ya karɓe jihar Legas.

Shugaba Bola Tinubu da Atiku Abubakar.
"Ban Taba Cin Amanar Shugaba Bola Tinubu Ba" Atiku Ya Maida Martani Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar PDP a zaɓen 2023 ya ce shi ne ya yi duk mai yuwuwa wajen ganin cewa jihar Legas ba ta faɗa guguwar tsunamin siyasa ba a 2003.

Kara karanta wannan

Takardun Karatun Tinubu: Jam'iyyar APC Ta Fusata, Ta Yi Wa Atiku Wankin Babban Bargo

Jaridar The Nation ta rahoto cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya yi wannan furucin ne a wurin taron manema labarai da ya kira a Abuja ranar Alhamis.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamansa Atiku ya ce:

"Wadanda suka san abinda ya faru a lokacin, za ku tuna cewa a shekarar 2003, jam'iyyar PDP ta kwace dukkan jihohin Kudu maso Yamma, ban da jihar Legas."
“Ni na shiga na tsaya tsayin daka tsakanin Obasanjo da shi (Tinubu) na ce a’a, ba za a kwace Legas ba. Ka kyale ta kuma ya haƙura ya kyale."
"To a haka wane ne yake bin wani bashi? Ni ko Bola Ahmed Tinubu? Na musanta cewa na daɓa wa Tinubu wuka ta baya. Akwai sauran abubuwan da ba zan so in taɓo su ba."

Atiku ya ƙara da cewa tuntuni shi da Tinubu suka raba gari a siyasance bayan da tsohon gwamnan jihar Legas ya so ya zama abokin takararsa a shekarar 2007, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Gwamnan Benue Ya Bayyana Adadin Kudin Fansan Da Aka Biya Kafin Sakin Kwamishinansa Da Aka Sace

Atiku Abubakar Ya Gindaya Sharaɗi 1 Rak Da Zai Sa Ya Daina Yaƙar Shugaba Tinubu

Kuna da labarin cewa Atiku Abubakar ya bayyana abinda zai kawo ƙarshen faɗansa da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Yayin da yake jawabi ga manema labarai a Abuja ranar Alhamis, 5 ga watan Oktoba, 2023, Atiku ya ce bai shirya ja da baya a faɗan da ya kinkimo ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262