Majalisar Dattawa Ta Gayyaci Hafsoshin Tsaro Kan Sace Daliban Jami'a

Majalisar Dattawa Ta Gayyaci Hafsoshin Tsaro Kan Sace Daliban Jami'a

  • Majalisar dattawa ta cimma matsayar gayyato manyan hafsoshin tsaro a kan batun garkuwa da ɗaliban jami'o'i
  • Sanata Abdulaziz Musa Yar’Adua ne ya gabatar da kudiri inda ya ja hankalin sauran sanatoci kan sace ɗalibai mata a FUGUS
  • Bayan tattake wuri, majalisar ta ce zata sanya ranar ta gayyaci hafsoshin tsaro su bayyana a gabanta domin su yi ƙarin haske

FCT Abuja - Majalisar dattawa, a ranar Alhamis, ta yanke shawarar gayyatar dukkan shugabannin jami’an tsaro saboda karuwar garkuwa da daliban jami’a a sassan Najeriya.

Daily Trust ta ce hakan ya biyo bayan kudirin da Sanata Abdulaziz Musa Yar’Adua (Katsina ta tsakiya) ya gabatar wanda ya jawo hankalin sauran abokan aikinsa a zaman yau.

Majalisar dattawa ta yi magana kan sace daliban jami'o'i.
Majalisar Dattawa Ta Gayyaci Hafsoshin Tsaro Kan Sace Daliban Jami'a Hoto: @SenateNGR
Asali: Facebook

Sanata Yar'adua ya ja hankalin majalisar dattawa kan sace ɗalibai mata 5 a jami'ar gwamnatin tarayya da ke garin Dutsin-ma (FUGUS) da sanyin safiyar ranar Laraba.

Kara karanta wannan

'Dan Majalisar Tarayya Ya Kai Koken 'Yan Arewa, Ya Faɗi Hanyar Kawo Karshen Matsalar Tsaro

Harin ya faru ne kwanaki 12 bayan wasu ‘yan bindiga sun shiga dakunan kwanan dalibai uku na Jami’ar Tarayya Gusau da ke Jihar Zamfara, inda suka yi garkuwa da dalibai mata 24.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata ‘Yar’Adua ya ce irin wadannan abubuwan da suka faru na garkuwa da mutane a 'yan kwanakin nan, sun jefa jami’ar da ɗalibai cikin firgici.

Ya kuma nuna damuwarsa kan yadda yawaitar garkuwa da mutane domin neman kudin fansa ya zama ruwan dare a kullum da mako-mako a manyan garuruwa da ƙauyukan yankin Arewa maso Yamma.

Wane mataki majalisar dattawan za ta ɗauka?

Bisa damuwa da karuwar satar daliban, Majalisar Dattawa ta yanke shawarar sanya ranar gayyato hafsoshin tsaro domin su yi mata jawabi kan sace daliban da kuma kokarin da suke na daƙile lamarin.

Haka kuma ta bukaci hukumomin tsaron Najeriya da su kara ƙaimi wajen ganin an sako wadannan ɗaliban da aka sace ba tare da bata lokaci ba, Arise TV ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Sanatoci Sun Tsige Shugaban Majalisar Dattawa Daga Muƙaminsa Kan Abu 1? Gaskiya Ta Bayyana

Majalisar ta yi kira ga sojoji da sauran jami’an tsaro da su gudanar da wani samame na musamman domin fatattakar ‘yan bindiga a shiyyar Arewa maso Yamma.

Tsohuwar Mai Tsawatarwa a Majalisar Wakilai, Binta Bello, Ta Fice Daga PDP

A wani rahoton na daban kuma Fatima Binta Bello, 'yar majalisar da ta wakilci mazabar Kaltungo/Shongom a majalisar wakilan tarayya ta 8 ta fice daga PDP.

Tsohuwar mai tsawatarwa ta marasa rinjaye a majalisar wakilai ta tabbatar da haka ne a wata wasiƙa da ta fito ranar Alhamis, 5 ga watan Oktoba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262