Atiku: Gani Fawehinmi Ne Ya Karafafa Min Gwiwa Na Binciki Takardun Tinubu
- Alhaji Atiku Abubakar, Dan Takarar Shugaban Kasa na Jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ya kira taron menama labarai a yau Alhamis
- Tsohon Mataimakin Shugaban Kasar ya ce marigayi Gani Fawehinmi shine ya karfafa masa gwiwa domin cigaba da bincikar takardun karatun Bola Tinubu
- A ranar 7 ga watan Oktoban 1999, Fawhinmi ya shigar na kara kotu na neman a tilastawa jami'an tsaro bincikar takardun Tinubu
Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Dan Takarar Shugaban Kasa na Jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ya ce marigayin lauya mai kare hakkin biladama, Gani Fawehinmi ne ya karfafa masa gwiwa game da zurfafa bincike kan takardun karatun Shugaba Bola Tinubu.
Atiku ya shigar da kara kan Shugaba Tinubu bisa takardun karatunsa a Jami'ar Jihar Chicago da ke Amurka.
Ya nemi takardun domin yin amfani da su matsayin hujja na cewa Tinubu ya gabatar da takardun bogi wa INEC.
Zargin gabatar da takardun bogin na cikin abubuwan da kotun sauraron karar zaben shugaban kasa ta yi watsi da shi cikin karar da Atiku ya shigar na kallubalantar nasarar Tinubu.
Duk da hukuncin kotun, Atiku bai yi watsi da karar da ya shigar a kotun Amurka ba, yana fatan samun takardun Tinubu don yin amfani da su matsayin hujja a kotun koli.
Ya yi ikirarin cewa akwai alamomin tambaya a satifiket din da Tinubu ya mika wa INEC wanda hakan ya kamata yasa a soke halarcin takararsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A jawabin da ya yi yayin taron manema labarai kai tsaye a ranar Alhamis da wakilin Legit Hausa ya bibiya, ya ce bai kamata jami'an tsaro su dauki watanni ba domin tantance takardun yan takarar babban mukami.
Atiku: Gani Fawehinmi ne ya karfafa min gwiwa na binciki takardun Tinubu
Atiku ya ce:
"Mutuncin Najeriya na iya tubuwa. Ni mutum ne wanda ya yarda da dimokradiyya kuma dan kasa mai kaunar kasarsa.
"Dole in gode wa lauyoyinmu na gida da waje, saboda taimakawa da suka yi wurin fayyace wannan batun da aka shafe shekaru kimanin hamsin ana fama.
"Marigayin lauya mai rajin kare hakkin bil-adama Gani Fawehinmi, ya wanke mu. Yanzu zai huta bayan ganin aikin da ya fara shekaru 23 da suka shude bai gushe ba."
Dakaci karin bayani ...
Asali: Legit.ng