Kotun Zabe Ta Tsige Dan Majalisar Labour Party, Ta Bai INEC Sabon Umurni

Kotun Zabe Ta Tsige Dan Majalisar Labour Party, Ta Bai INEC Sabon Umurni

  • An soke nasarar zaben Honourable Bright Ngene na jam'iyyar Labour Party a jihar Enugu
  • Kotun sauraron kararrakin zaben majalisar dokokin jiha ta tsige Ngene a ranar Laraba, 13 ga watan Satumba
  • Saboda haka kotun ta yi umurnin sake sabon zabe a mazabar Enugu ta kudu cikin kwana 90

Jihar Enugu - A ranar Laraba, 13 ga watan Satumba ne kotun sauraron kararrakin zaben majalisar dokokin jiha da ke zama a jihar Enugu, ta soke ayyana Honourable Bright Ngene na Labour Party a matsayin dan majalisar jiha mai wakiltar mazabar Enugu ta Kudu.

Kotun zabe ta tsige dan majalisar LP a jihar Enugu
Kotun Zabe Ta Tsige Dan Majalisar Labour Party, Ta Bai INEC Sabon Umurni Hoto: The Cable
Asali: Facebook

Da yake soke zaben, kwamitin mutum uku karkashin jagorancin A. M. Abubakar ya bayar da umarnin sake gudanar da sabon zabe a mazabar Enugu ta Kudu cikin kwanaki 90, kamar yadda Sahara Reporters ta rahoto.

Kara karanta wannan

PDP Na Kara Shanyewa Yayin da Kotun Zabe Ta Tsige Sanata 1 Da Yan Majalisar Wakilai 3

Dalilin da yasa kotu ta tsige dan majalisar Labour Party Ngene

Da take fadin dalilin soke zaben, kotun zaben ta ce hakan ya kasance ne saboda adadin kuri'un da aka ce wanda ya lashe zaben ya samu bai kai adadin na wadanda aka hana yin zabe a mazabar ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Saboda haka, kotun ta ce hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta yi kuskure da ta ayyana Bright Ngene a matsayin wanda ya lashe zaben.

Ta kara da cewar da kamata ya yi ace hukumar zaben ta ayyana zaben a matsayin wanda bai kammalu ba sannan a sake sabon zabe a wuraren da ba a gudanar da zaben ba saboda tazarar da ke tsakanin manyan yan takarar.

Kotun zabe ta tsige yan majalisar tarayya na PDP 4 a jihar Filato

Kara karanta wannan

Jerin Sanatocin APC 4 Da Kotun Zabe Ta Tsige Da Kuma Dalili

A wani labarin, mun ji cewa jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta hadu da gagarumin cikas a jihar Filato yayin da kotun sauraron kararrakin zaben yan majalisun tarayya da ke zama a Jos ta tsige yan majalisarta na tarayya guda hudu.

A zamanta na ranar Laraba, 13 ga watan Satumba, kotun zaben ta soke zaben yan majalisa guda hudu saboda rashin tsari, Channels TV ta rahoto.

Kwamitin mutum uku karkashin mai shari'a Mohammed Tukur, sun yanke hukunci cewa ba a bi tsarin da ya kamata ba wajen zabar yan takarar na PDP a jihar saboda jam'iyyar bata da tsari a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng