PDP Na Kara Shanyewa Yayin da Kotun Zabe Ta Tsige Sanata 1 Da Yan Majalisar Wakilai 3

PDP Na Kara Shanyewa Yayin da Kotun Zabe Ta Tsige Sanata 1 Da Yan Majalisar Wakilai 3

  • Jam'iyyar PDP a jihar Filato ta gamu da gagarumin cikas yayin da ta rasa daya daga cikin sanatocinta da mambobinta na majalisar wakilai uku
  • Kwamitin mutum uku karkashin jagorancin Mai shari'a Mohammed Tukur sun yanke cewa ba a bi tsarin da ya kamata ba wajen zabar yan majalisar
  • Bayan hukuncin kotun, yan takarar majalisar wakilai biyu daga Labour Party da daya daga APC sun ci gajiyar hukuncin, yayin da tsohon gwamna Simon Lalong ya lashe kujerar sanata

Jos, Plateau - Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta hadu da gagarumin cikas a jihar Filato yayin da kotun sauraron kararrakin zaben yan majalisun tarayya da ke zama a Jos ta tsige yan majalisarta na tarayya guda hudu.

A zamanta na ranar Laraba, 13 ga watan Satumba, kotun zaben ta soke zaben yan majalisa guda hudu saboda rashin tsari, Channels TV ta rahoto.

Kara karanta wannan

Jerin Sanatocin APC 4 Da Kotun Zabe Ta Tsige Da Kuma Dalili

Kotun zabe ta tsige yan majalisar tarayya na PDP 4
PDP Na Kara Shanyewa Yayin da Kotun Zabe Ta Tsige Sanata 1 Da Yan Majalisar Wakilai 3 Hoto: PDP Update
Asali: Twitter

Kwamitin mutum uku karkashin mai shari'a Mohammed Tukur, sun yanke hukunci cewa ba a bi tsarin da ya kamata ba wajen zabar yan takarar na PDP a jihar saboda jam'iyyar bata da tsari a jihar.

Kotun zabe ta tsige yan majalisa na PDP guda hudu a Filato

  1. Peter Gyendeng: Dan majalisa mai wakitar mazabar Barkin-Ladi/Riyom a majalisar wakilai
  2. Musa Bagos: Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Jos ta Kudu/Jos ta Gabas
  3. Beni Lar: Dan majalisa mai wakiltan mazabar Langtang ta arewa/Langtang ta kudu
  4. Napoleon Bali: Sanata mai wakiltan Filato ta Kudu

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ga jerin wadanda suka ci moriyar hukuncin a kasa:

  1. Fom Dalyop: Dan takarar Labor Party a zaben mazabar Barkin-Ladi/Riyom
  2. Ajang Alfred Iliya: Dan takarar Labor Party a zaben mazabar Jos ta Kudu/Jos ta Gabas
  3. Vincent Bulus Venman: Dan takarar jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a mazabar Langtang ta arewa/Langtang ta kudu
  4. Simon Lalong: Ministan kwadago mai ci kuma tsohon gwamnan jihar ya samu kujerar sanata mai wakiltan Filato ta Kudu

Kara karanta wannan

"Ba Zata Sabu Ba" Dan Majalisar Tarayya Na PDP Da Kotu Ta Tsige Ya Fusata

Sai dai kuma, jam'iyyar PDP ta nuna rashin gamsuwa da hukuncin, wanda ya yi karo da hukuncin wani kwamiti a kotrun zaben.

Jerin sanatocin APC 4 da kotun zabe ta tsige da dalili

A wani labarin kuma, mun ji cewa jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki ta lashe mafi rinjayen kujeru a majalisar dattawa a zaben majalisar dokokin tarayya da aka yi a ranar 25 ga watan Fabrairu.

Kasancewarta jam'iyyar da ta fi yawan sanatoci a zauren majalisar dattawan, APC ta karbe mukaman shugabanci a majalisar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng