Adamawa: Ban Taba Aje Biliyan 1 a Asusun Banki Ba a Matsayin Gwamna, Ngilari

Adamawa: Ban Taba Aje Biliyan 1 a Asusun Banki Ba a Matsayin Gwamna, Ngilari

  • Tsohon Gwamnan Adamawa ya tabbatar da cewa bai taɓa samun kuɗin da suka kai Naira biliyan ɗaya ba a asusunsa har ya gama mulki
  • A kwanakin bayan an ji Bala Ngilari na cewa zai iya faɗuwa ya suma idan ya ga kuɗi Biliyan N1bn a cikin asusun bankinsa
  • Sai dai a wata hira da ya yi ranar Laraba, ya ce ya faɗi haka ne da wasa amma mutane suka ɗauka da gaske

Adamawa - Tsohon gwamnan jihar Adamawa, Bala Ngilari, ya jaddada ikirarinsa cewa bai taɓa aje Naira biliyan ɗaya ba a Asusun bankinsa har ya sauka daga mulki.

Ngilari ya ƙara tabbatar da kalamansa ne yayin da ya bayyana a shirin Sunrise Daily na gidan talabijin na Channels tv ranar Laraba, 13 ga watan Satumba, 2023.

Kara karanta wannan

Shin Da Gaske CBN Na Son Sauya Fasalin Naira Domin Ta Dawo Daidai Da Dala? Bayanai Sun Fito

Tsohon gwamnan jihar Adamawa, Bala Ngilari.
Adamawa: Ban Taba Aje Biliyan Daya a Asusun Banki Ba a Matsayin Gwamna, Ngilari Hoto: channelstv
Asali: UGC

Ya sake jaddada wannan ikirari ne a lokacin da aka tambaye shi kan kalaman da ya yi cewa zai iya suma idan ya ga Naira biliyan daya a asusun sa a wata hira da aka yi da shi kwanan nan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shin da gaske bai taɓa samun N1bn ba?

Tsohon gwamnan ya ce:

"Za a iya tabbatar da wannan, ana iya bincika asusuna, shekaru takwas da suka wuce babu lokacin da na taba samun kuɗi da suka kai Naira biliyan ɗaya a cikin asusuna."

A cewarsa, ya samu damarmaki da yawa da zai iya tara irin waɗan nan kudi a asusunsa, amma ka’idojin da’a da kuma nauyin da ya rataya a kansa ya sanya ya bi hnyar da ta dace wajen sarrafa kudaden jihar.

“Wannan ba ya na nufin ban samu damar da zan samu irin wannan kudin ba lokacin da nake gwamna. Kawai ban zaɓa wa kaina bin wannan hanyar ba kuma ku tuna ni lauya ne, na daɗe a sha'anin doka."

Kara karanta wannan

Tinubu Na Shirin Daina Amfani Da Naira, a Koma Amfani Da Dala a Najeriya?, Gaskiya Ta Bayyana

Tsohon gwamnan ya ƙara da bayanin cewa kalaman da ya yi a baya na suma wasa ne da mutane suka dauka da gaske har aka yi ta yaɗa wa, Daily Trust ta rahoto.

Ya kuma bayyana cewa ya yafe wa waɗanda suna shiga suka fita har hukumar yaƙi da rashawa EFCC ta kama shi ta kai Kotu aka ɗaure shi.

Jam'iyyar APC Ta Rasa Kujerun Sanata 2 a Jihar Delta

A wani rahoton kuma Kotun zaɓe ta bayyana zaben Sanatan mazaɓar jihar Delta ta tsakiya na APC a matsayin wanda bai kammalu ba.

Kwamitin alƙalai uku na Kotun ƙarƙashin jagorancin mai shari'a W.I. Kpochi, ya ba da umarnin ƙarisa zaɓe a rumfunan zaɓe 48 a ƙananan hukumomi 4 daga cikin 8 na mazaɓar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262