Kotun Zabe Ta Ayyana Zaben Ɗan Majalisar Tarayya A Matsayin Wanda Bai Kammalu Ba
- Kotun zaɓen NASS mai zama a jihar Legas ta soke sakamakon zaben ɗan majalisar tarayya mai wakiltar mazaɓar Eto Osa
- Da take yanke hukunci, Kotun ta ayyana zaben a matsayin wanda bai kammalu ba kuma ta umarci INEC ta shirya sabo
- INEC ta ayyana ɗan takarar Labour Party a matsayin wanda ya lashe zaɓe, amma ɗan takarar PDP da na APC suka nufi Kotu
Lagos - Kotun sauraron ƙararrakin zaben yan majalisar tarayya mai zama a jihar Legas ta rushe nasarar Mista Thaddeus Atta na LP a matsayin zaɓaɓɓen mamba mai wakiltar mazaɓar Eto Osa.
Channels tv ta tattaro cewa yayin yanke hukunci ranar Litinin da daddare, Kotun ta ayyana zaɓen mazaɓar Eto Osa ta tarayya a matsayin wanda bai kammalu ba (Inconclusive).
Ta kuma umarci hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta gudanar da zaɓen cike gurbi a rumfunan zaɓe 33 da zabe bai gudana ba cikin kwanaki 90 masu zuwa.
Ɗan majalisar ya maida martani
Da yake maida martani kan hukuncin da Kotu ta yanke a shafinsa na manhajar X, wanda aka fi sani da Tuwita, Atta ya ce wannan ba wani abun damuwa bane, inda ya ce Kotu ba ta tsige shi ba.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya ce:
“Kotu ta ba da umarnin sake gudanar da zabe (karishen zabe) a rumfunan zabe 32 ba a yi zabe ba."
"Za mu ci gaba da yi wa Etiosa aiki. Ina kira ga masu kaɗa kuri'a a mazaɓata da su kwantar da hankulansu saboda ba mu girgiza ba. Za mu shawo kan wannan tare."
Bankole Wellington (Banky W) na PDP da ya zo na biyu da ɗan takarar jam’iyyar APC, Ibrahim Babajide Obanikoro (IBO) duk sun shigar da karar kalubalantar zaben ranar 25 ga watan Fabrairu.
INEC ta bayyana Atta wanda ya samu kuri’u 24,075 a matsayin wanda ya lashe zaben, yayin da Banky W da IBO suka samu kuri’u 18,668 da 16,901, bi da bi.
"Ku Ja Kunnen Wike" Tsagin Atiku Ya Maida Martani, Ya Aike da Sako Ga PDP
A wani rahoton na daban kuma Rigingimun cikin gida da suka addabi babbar jam'iyyar adawa a Najeriya PDP tsakanin Atiku da Wike ya ɗauki sabon salo.
Tsagin tawagar G5 ƙarƙashin tsohon gwamnan Ribas, Nyeson Wike, ya yi kira da a dakatar da Atiku Abubakar da Aminu Tambuwal daga jam'iyyar PDP.
Asali: Legit.ng