Abia: Kotu Ta Tsige 'Yan Majalisun Tarayya Biyu Na LP, Ta Ba APC da APGA Nasara
- Jam'iyyar Labour Party ta ƙara rasa kujerun 'yan majalisar wakilan tarayya a jihar Abia da ke Kudu maso Gabas
- Kotun sauraron ƙararrakin zaben NASS ta tsige 'yan majalisun guda biyu ranar Litinin, ta bayyana waɗanda suka ci zaɓe
- Wannan hukunci na zuwa ne ƙasa da mako ɗaya bayan Peter Obi ya yi rashin nasara a ƙarar da ya kalubalanci nasarar Bola Tinubu
Jihar Abia - Kotun sauraron ƙorafe-korafen zaɓen 'yan majalisun tarayya (NASS) ta tsige ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Arochukwu/Ohafia, Ibe Okwara, na Labour Party (LP)
Channels tv ta tattaro cewa Kotun zaɓen NASS mai zama a Umuahia, babban birnin jihar Abiya ta yanke wannan hukunci ne ranar Litinin, 11 ga watan Satumba.
Bayan sauke ɗan majalisar, Kotun ta ayyana ɗan takarar APC, Dan Okeke, a matsayin wanda ya lashe zaɓen mamban majalisar tarayya a mazaɓar ranar 25 ga watan Fabrairu.
Kotu Ta Rushe Nasarar Ɗan Majalisar Tarayya a Jihar APC, Ta Ayyana Zaɓen a Matsayin Wanda Bai Kammalu Ba
Yayin da hukumar zaɓe ta ƙasa mai zaman kanta (INEC) ta ayyana ɗan takarar LP A matsayin wanda ya ci zaɓe, Okeke ya nuna rashin gamsuwa da hakan kana ya nufi Kotu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Mista Okeke ya yi musun cewa nasarar ɗan takarar LP ba ta cika sharuɗɗan da kundin dokokin zaɓen Najeriya ya tanada ba, bisa haka ya roƙi Kotu ta rushe zaɓen.
Watanni bayan shigar da ƙarar, kwamitin Alƙalai uku ƙarƙashin mai shari'a Adeyinka Aderegbegbe, ya amince da buƙatarsa kuma ya yanke hukuncin cewa Ibe bai cika sharuɗɗa ba.
Haka nan ya ayyana ɗan takarar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓe kana ya umarci INEC ta janye Satifiket ɗin da ta bai wa Ibe, ta ba Okeke sabo, The Nation ta rahoto.
Kotu ta bai wa jam'iyyar APGA nasara
Haka zalika, wata kotun sauraron ƙarar zaben 'yan majalisar dokokin da ke zamanta a Umuahia ta kori dan majalisar mai wakiltar mazabar tarayya ta Abia ta Arewa/Kudu na LP.
Kotun ta bayyana Alex Ikwechegh na jam’iyyar APGA a matsayin wanda ya lashe zaben mazaɓar a watan Fabrairu.
Kwara: PDP Ta Nada Mataimakin Shugaban Jam'iyya, Sakatare da Wasu 2
A wani rahoton kuma Jam'iyyar PDP ta naɗa sabbin shugabanni guda huɗu a jihar Kwara bayan murabus din wasu a kwanakin baya.
PDP ta naɗa mataimakin shugabanta na jiha, Sakatare, sakataren watsa labarai da kuma mukaddashin shugaban matasa.
Asali: Legit.ng