Kotu Ta Tabbatar Da Nasarar Sanata Abba Moro Na Jam'iyyar PDP
- Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen ƴan majalisar tarayya a jihar Benue ta tabbatar da nasarar Sanata Abba Moro na jam'iyyar PDP
- Kotun ta yi watsi da ƙarar da ɗan takarar jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Mista Daniel Onjeh ya shigar
- Mai shari'a Ory Zik-Ikeorha ta yi hukunci cewa mai shigar da ƙarar ya kasa kawo gamsassun hujjoji kan ƙarar da ya shigar
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Benue - Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen ƴan majalisar tarayya a jihar Benue ta tabbatar da nasarar sanatan Benue ta Kudu, Sanata Abba Moro na jam'iyyar PDP.
Kotun mai alƙalai uku wacce mai shari'a Ory Zik-Ikeorha take jagoranta ta yi fatali da ƙarar da Mista Daniel Onjeh na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), ya shigar yana ƙalubalantar nasarar Sanata Abba Moro.
Idan za a iya tuna wa dai hukumar zaɓe ta bayyana Sanata Abba Moro a matsayin wanda ya lashe zaɓen sanatan Benue ta Kudu wanda aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.
Dan Majalisar Jam'iyyar Labour Party Da Kotu Ta Kora Ya Yi Martani, Ya Bayyana Matakin Dauka Na Gaba
Rashin gamsuwa da hakan ya sanya Mista Onjeh ya shigar da ƙara a kotun inda ya yi zargin cewa Sanata Moro bai lashe zaɓen da yawan ƙuri'u ba, sannan ba a gudanar da zaɓen bisa tanadin sabuwar dokar zaɓe ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kotu ta zartar da hukuncinta
Da take yanke hukunci kan ƙarar a ranar Lahadi, 10 ga watan Satumba a birnin Makurdi, mai shari'a Zik-Ikeorha, ta yi hukunci cewa shaidun da mai shigar da ƙarar ya kawo sun yi kaɗan su tabbatar da zargen-zargen da yake yi.
Mai shari'ar ta kuma yi nuni da cewa shaidun da masu shigar da ƙarar suka gabatar sun yi rauni sosai.
Mai shari'ar ta yi watsi da ƙarar sannan ta tabbatar da nasarar Sanata Abba Moro a matsayin sanatan Benue ta Kudu, rahoton Daily Post ya tabbatar.
Lauyoyi sun yi martani kan hukuncin kotun
Da yake martani kan hukuncin kotun, lauyen Onjeh, Mista Tunde Oso, ya bayyana cewa zai tattauna da wanda yake karewa kafin yanke shawarar matakin da za su ɗauka na gaba.
A na sa ɓangaren, lauyan Moro, Mista Rafael Adakole ya bayyana cewa kotun ta tabbatar da zaɓin da mafi yawan al'ummar Benue ta Kudu suka yi ne ta hanyar yin adalci a shari'ar.
Kotu Ta Tabbatar Da Nasarar Dan Majalisar APC
A wani labarin na daban, kotun zaɓe ta tabbatar da nasarar ɗan majalisar APC mai wakiltar Ado/Okpokwu/Ogbadibo, Philip Agbese.
Kotun ta yi fatali da ƙarar da abokan takararsa suka shigar suna ƙalubalantar nasarar da ya samu a zaɓen ranar 25 ga watan Fabrairu.
Asali: Legit.ng