Kotu ta Dawo da Rabiu Kwankwaso Cikin NNPP Bayan An Fatattake Shi Daga Jam’iyya

Kotu ta Dawo da Rabiu Kwankwaso Cikin NNPP Bayan An Fatattake Shi Daga Jam’iyya

  • Wasu ‘ya ‘yan jam’iyyar NNPP sun yi karar ‘ya ‘yansu a sakamakon rikicin cikin gidan da ake yi
  • A dalilin haka kotu ta soma rusa korar da aka yi wa ‘dan takaran 2023, Rabi’u Musa Kwankwaso
  • Kotu ta ce INEC ta daina sauraron bangaren Boniface O. Aniebonam da ya kafa jam’iyyar adawar

Kano - Wata babbar Kotu da ke zama a Jihar Kano ta soke korar da jam’iyyar hamayya ta NNPP ta yi wa Rabi’u Musa Kwankwaso.

A yammacin Talata, rahoto ya zo daga Aminiya cewa alkalin babban kotun da ke Kano ya zartar da hukunci a kan matakin jam’iyyar.

Mai shari’a Usman Na-Abba ya yanke hukuncin da ya wargaza matakin da wasu ‘yan tawaren jam’iyya mai kayan dadi su ka dauka.

Rabiu Kwankwaso
'Dan takaran NNPP, Rabiu Kwankwaso Hoto: @SaifullahiHon
Asali: Twitter

Rikicin cikin gidan NNPP

Kara karanta wannan

Jam’iyyar NNPP Ta Doke Abba Ganduje a Kotu a Karar Zaben ‘Dan Majalisa a Kano

Jam’iyyar NNPP ta shigar da kara a kotu, ta na karar wasu shugabanninta da ake rigima da su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wadanda ake kara sun hada da Boniface O. Aniebonam, Gilbert Agbo Major, Barista Tony Christopher Obioha da kuma Mark Usman.

Rahoton ya ce Ogini Olaposi, Hajia Rekia Zanlaga, Mark Usman, Umar A. Jubril da Adebanju Wasiu su na cikin wadanda ake tuhuma.

Na-Abba ya fara yanke hukuncin wucin-gadi ne kafin lokacin da za ayi zaman karshe.

NNPP: Kotu ta ba INEC umarni

Alkalin ya umarci hukumar zabe na kasa watau INEC da ta guji amincewa da duk abin da zai fito daga bangaren wadanda aka yi kara.

Ragowar jagororin na NNPP da aka maka a kotu su ne: Alhaji Tajudeen Adebayo, Alhaji Mamoh Garuba da AbdulRasaq Abdulsalam.

Akwai Abiola Henry Olarotimi, Injiniya Babayo Abdullahi Mohammed, Alhaji Ibrahim Yahaya, Chinonso Adiofu da Sunday Chukwuemek.

Kara karanta wannan

Yadda Shugaban Majalisar Wakilai Ya Rabawa Mutanensa Da 'Yan Adawarsa Mukamai

Baya ga Barista Jonathan Chineme Ibeogu, hukumar INEC ta na cikin wadanda ake shari’a da su yayin da rikicin cikin gidan ya cabe.

Kwankwaso ya na nan a NNPP

Ku na da labari NEC ta ce Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya na nan a matsayin ‘Dan jam’iyyar New Nigeria Peoples Party har gobe.

Majalisar koli ta Mallam Kawu Ali ta ce ‘dan takaranta na shugaban kasa a zaben 2023 shi ne fuskar NNPP, babu wanda zai kore shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng