"Kwankwaso Matsala Ne a Siyasa" Sabon Shugaban NNPP Na Shiyyar Kudu
- Rikicin jam'iyyar NNPP ya ƙara tsananta yayin da shugaban kudu ya tona cin amanar da Kwankwaso ya yi ana dab da zaɓen 2023
- Sabon shugaban NNPP na shiyyar Kudu maso Yamma, Alhaji Wasiu Ajirotutu, ya ce Kwankwaso ba abinda yarda bane a siyasa
- Ya ƙalubalanci tsohon gwamnan Kanon ya fito ya musanta cewa ya gana da Tinubu kwana huɗu kafin zaɓe
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Sabon mataimakin shugaban jam'iyyar NNPP na shiyyar Kudu maso Yamma wanda aka zaɓa kwanan nan, Alhaji Wasiu Ajirotutu, ya caccaki tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso.
Sabon mataimakin shugaban jam'iyyar ya ayyana Kwankwaso, ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar NNPP a zaben 2023 da mutum mai son kai da ɗaukar alhaki a siyasa.
Ya kuma kalubalanci Kwankwaso ya fito bainar jama'a ya musanta zargin cewa ya gana da ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, Bola Tinubu, kwana huɗu gabanin zaɓe.
Jagoran NNPP na shiyyar ya yi wannan kalamai ne a wata sanarwa da aka raba wa manema labarai ranar Litinin, 24 ga watan Satumba, 2023, kamar yadda Punch ta tattaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya jaddada cewa ganawar da Kwankwaso ya yi da shugaba Tinubu kwanaki kaɗan kafin fafata zaɓen shugaban ƙasa, zagon ƙasa ne da cin amanar yardar da NNPP ta masa.
Ajirotutu ya zama Shugaban NNPP a Kudu maso Yamma a ranar Talata ta makon jiya bayan kwamitin amintattu ya rushe NWC na tsagin Kwankwasiyya tare da dakatar da Kwankwaso tsawon watanni shida.
Yadda Kwankwaso ya ci amanar NNPP
Da yake martani kan dakatar da Kwankwaso, Mista Ajirotutu ya yi bayanin cewa tsohon gwamnan Kano ya yi amfani da tsarin NNPP ne wajen cimma son zuciyarsa.
Ya ƙara da cewa ya shirya ɗaga darajar jam'iyyar NNPP mai kayan marmari ta zama gagara misali a shiyyar Kudu maso Yammacin Najeriya, Vanguard ta rahoto.
Tsohon Sanata Ya Yi Wa Atiku Wankin Babban Bargo Kan Kalubalantar Nasarar Tinubu, Ya Ba Shi Wata Muhimmiyar Shawara
A kalamansa, ya ce:
"Kwankwaso ya yaudare mu kamar yana cikin yan takarar shugaban ƙasa alhali a zuciyarsa yana da wata manufa amma ba takarar gaske yake yi ba."
Shugaba Bola Tinubu Ya Gana da Manyan Hafsoshin Tsaro A Aso Villa
A wani labarin na daban kuma Shugaba Tinubu ya yi ganawa mai matukar muhimnanci da hafsoshin tsaro a Villa da ke Abuja.
Hafsoshin tsaron zasu yi wa Tinubu bayani kan halin da ake ciki yayin da ya cika kwanaki 10 da hawa kan madafun iko.
Asali: Legit.ng