Zaben 2023: Prophet Barnabas Ya Yi Hasashen Yadda Peter Obi Zai Zama Shugaban Kasa
- Har yanzu Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party (LP) a zaɓen 2023, yana ƙalubalantar nasarar Shugaba Tinubu a kotu
- Wani fasto a jihar Benue, Prophet Barnabas ya bayyana wani labari mai matuƙar daɗi ga 'Obidients' magoya bayan Peter Obi
- Malamin addinin ya bayyana cewa Peter Obi zai zama shugaban ƙasar Najeriya, sannan ya yi bayanin yadda hakan zai faru
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Zaki-Biam, jihar Benue - Fasto Barnabas na cocin Mercy and Grace Deliverance Ministry a ƙaramar hukumar Ukum ta jihar Benue, ya bayyana cewa Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar zai zama shugaban ƙasa.
Faston ya yi bayanin cewa Peter Obi zai zama shugaban ƙasa ne ta hanyar da mutane ba su taɓa zato ba.
A cewa Fasto Barnabas, Obi shi ne wanda ya cancanta ya ɗare kujerar shugaban ƙasa a Aso Villa.
"Ubangiji yana da shiri a kan Obi", fasto Barnabas
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya bayyana cewa ubangiji ne ya tsaro cewa ɗan takarar na jam'iyyar LP ba za a bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa ba na ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.
Faston dai ya bayyana hakan ne a cikin wani bidiyo da ya sanya a shafinsa na Youtube.
A kalamansa:
"Peter Obi zai shiga ta inda ba ku taɓa zato ba."
"Jagaban (yana nufin shugaban ƙasa Bola Tinubu) ba zai kammala wa'adin mulkinsa ba, Peter Obi zai karɓe mulki."
"Mutane ba za su ankara ba lokacin da Peter Obi zai shiga. Za su riƙa tambaya: 'ta ya hakan ta kasance?"
"Kujerar shugaban ƙasar nan mallakin Peter Obi ce. Da a ce ya yi nasara a karon farko, da ni da ku da duk mun mutu. Haka shi ne dalilin da ya sanya ubangiji ya sanya wanda bai dace ba saboda a samu zaman lafiya.
"Yanzu, ubangiji zai sauya wanda bai dacen ba da wanda ya dace. Wannan aikin ubangiji ne."
Fasto Ya Hango Nasarar Peter Obi
A wani labarin kum, wani fitaccen fasto ya bayyana cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party (LP), Peter Obi, yana dab da cikin burinsa.
Fasto Kingsley Okwuwe ya bayyana cewa ya samu sabon wahayin cewa Peter Obi zai zama shugaban ƙasa.
Asali: Legit.ng