Rikicin APC: Ganduje Ya Yi Alƙawarin Shawo Kan Rigima Kan Kujerun Mambobin NWC

Rikicin APC: Ganduje Ya Yi Alƙawarin Shawo Kan Rigima Kan Kujerun Mambobin NWC

  • Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya sha alwashin warware rikicin da ya kunno kai kan muƙaman mambobin kwamitin NWC
  • Saɓani ya kunno kai a jam'iyyar mai mulki bayan sanar da sunayen mutanen da zasu cike gurbin da babu kowa a NWC na ƙasa
  • Bayan ganawa da gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi, Ganduje ya ce za su warware matsalar cikin ruwan sanyi

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT Abuja - Shugaban jam'iyyar APC ta ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya tabbatar wa 'ya'yan jam'iyyar cewa nan bada jimawa ba za a shawo kan matsalolin cikin gida.

Ganduje wanda ya kira rikicin da, "matsalar iyali," wanda ya ɓarke bayan sanar da sabbin mambobin kwamitin gudanarwa (NWC), ya ce zasu warware komai cikin ruwan sanyi.

Shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje.
Rikicin APC: Ganduje Ya Yi Alƙawarin Shawo Kan Rigima Kan Kujerun Mambobin NWC Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

Channels tv ta rahoto cewa shugaban APC ya yi wannan furucin ne jim kaɗan bayan ganawa da gwamna Yahaya Bello na Kogi ranar Alhamis a birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Tsohon Hadimin Buhari Ya Yabawa Kokarin Gwamna Abba Gida Gida a Jihar Kano

Tsohon gwamnan jihar Kano ya shaida wa manema labarai cewa duk wani saɓani da aka samu sakamakon naɗa mambobin NWC zasu zama tarihi nan gaba kaɗan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaban jam'iyyar APC ya jaddada yaƙinin cewa gwamnan Kogi, Yahaya Bello zai kawo wa jam'iyya mai mulki nasara a zaben gwamna mai zuwa ranar 11 ga watan Nuwamba, 2023.

A nasa ɓangaren, gwamna Bello ya jaddada goyon bayansa ga shugabancin jam’iyyar, inda ya ƙara da cewa APC za ta ci gaba da rike jihar da ke Arewa ta Tsakiya.

Rikici ya kunno kai a APC mai mulki

An samu ɓaraka a APC bayan sanar da sunayen waɗanda zasu maye gurbin wasu muƙamai a kwamitin ayyuka na ƙasa (NWC), Leadership ta ruwaito.

Rahotanni sun bayyana cewa gwamna Bello, da yan majlisun tarayya na jihar Kogi sun ziyarci babbar sakatariyar APC ta ƙasa bayan an yi watsi da sunan da suka aiko.

Kara karanta wannan

Sabon Rikici: Dakarun 'Yan Sanda Sun Mamaye Babbar Sakatariyar APC Ta Ƙasa, Bayanai Sun Fito

Haka zalika a ranar Laraba, ministar jin ƙai da yaye talauci, Betta Edo, ta ziyarci hedkwatar APC kan sabuwar shugaban mata da aka naɗa maimakon wacce ta turo.

Umahi: Zan Zauna da Masu Kamfanoni Domin Rage Farashin Siminti

A wani rahoton na daban Gwamnatin tarayya ta yi alkawarin tattauna wa da masu kamfanonin siminti domin rage farashin kayayyakinsu.

Ministan ayyuka, Sanata David Umahi, ya ce mafi akasarin 'yan kwangila sun yi ƙorafin cewa siminti ya fi tsada a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262