Yan Uwan Emefiele Sun Janye Karar Da Suka Shigar Kan DSS Da AGF

Yan Uwan Emefiele Sun Janye Karar Da Suka Shigar Kan DSS Da AGF

  • 'Yan uwan tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, sun sanar da janye ƙarar da suka shigar
  • Sun shigar da ƙarar jami'an DSS da kuma Attoni janar na ƙasa bisa zargin take haƙƙinsu da suka ce an yi
  • Mai shari'a E Okpe na babbar kotun tarayya ne ya sanar da hakan a yayin da yake watsi da ƙarar

FCT, Abuja - Mai shari'a E Okpe na babbar kotun tarayya, ya yi watsi da ƙarar da 'yan uwan tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele suka shigar a kan hukumar DSS da Attoni janar na Najeriya.

Hakan dai ya biyo bayan janye ƙarar da 'yan uwan na Godwin wato Emefiele George Emefiele da Okanta Emefiele, suka yi ta hanyar cike takardar tsame hannunsu daga shari'ar kamar yadda The Nation ta wallafa.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: An Samu Tangarda Wajen Gurfanar Da Emefiele a Kotu, Bayanai Sun Fito

'Yan uwan Emefiele sun janye ƙarar da suka shigar
'Yan uwan Godwin Emefiele sun janye ƙarar da suka shigar kan DSS da AGF. Hoto: Central Bank of Nigeria, Court of Appeal
Asali: Facebook

A kan menene 'yan uwan Emefiele suka shigar da ƙara?

'Yan uwan na Emefiele dai sun shigar da Attoni janar da DSS ƙara kan zargin tauye musu haƙƙi da suka ce anyi a yayin da ake gudanar da bincike kan Emefiele.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sun buƙaci kotu ta hana jami'an hukumar ta DSS daga kama su ko kuma tsare su a yayin da suke bincike kan laifukan da ake zargin Emefiele da aikatawa kamar yadda The Punch ta wallafa.

A zaman kotun na ranar Laraba ne lauyar da ke kare 'yan uwan na Emefiele Grace Ehusani ta shaidawa kotun cewa mutanen biyu sun nemi janye ƙarar da suka shigar, duk da dai ba ta bayyana dalilin hakan ba.

Kotu ta yi fatali da ƙarar ta hannun damar Emefiele

A baya Legit.ng ta yi rahoto kan watsi da ƙarar da Sa'adatu Yaro yana shigar kan hukumar jami'an tsaro na farin kaya wato DSS.

Kara karanta wannan

Aljeriya Na Ba Nijar Wutar Lantarki Kyauta Bayan Najeriya Ta Dai Na Ba Su? Gaskiya Ta Bayyana

Sa'adatu ta buƙaci kotun ta tursasa hukumar ta DSS sakar ma ta motocinta gami da bayar da ita beli.

Sa'adatu Yaro dai ita ce matar da ake tuhuma da baɗaƙalar zunzurutun kuɗaɗe har naira biliyan 6.9 tare da dakataccen gwamnan babban bankin Najeriya, Mista Godwin Emefiele.

Tinubu ya yi fatali da tsarin CBN na gwamnatin Buhari

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan watsi da tsohon tsarin da ake amfani da shi a babban bankin Najeriya (CBN) kan kuɗaɗe tun lokacin Muhammadu Buhari.

A watan Yulin shekarar 2021 ne CBN ya sanar da dakatar da sayarwa da 'yan kasuwar canji daloli da sauran kuɗaɗen ƙasashen waje.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng