An Bayyana Abun da Shugaban Kasa Tinubu Ya Fadawa Sabbin Ministoci 45 Da Aka Rantsar
- An bukaci sabbin ministocin tarayyar Najeriya da aka rantsar da su kama aiki nan take ba tare da bata lokaci ba
- Shugaba Bola Tinubu ya yi wannan kiran ne yayin da ya bukaci ministocin da su fifita ra'ayi da jin dadin al’ummar kasa gaba daya sama da na wani yanki ko jiha
- Shugaban Najeriyan ya kuma tunatar da sabbin ministocin cewa ba za su iya ba yan Najeriya kunya ba saboda haka yan kasar ba za su amshi kowani uzuri na gazawa ba
Abuja - A kokarinsa na sake zaburar da gwamnatinsa mai watanni uku, Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sake bayar da sabon umurni ga ministocin tarayyar Najeriya da aka rantsar.
A yayin bikin rantsar da ministocin a Abuja, a ranar Litinin, 21 ga watan Agusta, Tinubu ya bukace su da su bayar da fifiko ga ra'ayin kasa da al'ummarta, sannan su yi watsi ga karkata ga yanki ko jiha daya.
Jaridar The Guardian ta rahoto cewa Tinubu ya bukaci sabbin ministoci 45 da aka rantsar da su yi aiki wajen ganin an cimma manufofin da ke karfafa ajandar sabon fata na gwamnatinsa.
Da yake magana jim kadan bayan rantsar da sabbin mambobin majalisar zartarwa a cibiyar taro na fadar shugaban kasa Abuja, shugaban kasa Tinubu da yake jaddada hakkin da ya raya kan ministocin, ya ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Kai ba ministan wata jiha, mulkin mallaka, yanki ko wata kabilar kasar bane, kai ministan tarayyar Najeriya ne."
Tinubu ya ci gaba da bayyana cewa ya yi taka tsan tsan wajen zabar ministocin saboda tarin nasarorin da suka samu a bangarorin gwamnati da masu zaman kansu, rahoton Daily Trust.
Makinde da sauran yan G5 sun yi tsit kan mukamin Wike
A wani labarin kuma, mun ji cewa ga dukkan alamu, kungiyar G5 na gwamnonin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da suka yi zanga-zanga gabannin zaben shugaban kasa na 2023 sun daina aiki bayan uku daga cikinsu sun fita daga harkokin siyasa bayan zaben.
Hakan ya kasance ne yayin da shugaban kungiyar, Nyesom Wike, wanda ya kasance gwamnan jihar Ribas a lokacin, ya zama ministan Abuja a karkashin gwamnatin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki sannan tawagar G5 suka yi gum.
Asali: Legit.ng