Tinubu Ya Saka Labule Da Okorocha Da Uzodinma A Aso Rock, Bayanai Sun Fito
- Shugaba Bola Tinubu a halin yanzu yana ganawa da tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha da gwamnan Imo mai ci, Hope Uzodinma
- Duk da cewa ba a san dalilin ganawar ba amma Okorocha da Uzodinma sun isa Villa a ranar Alhamis 17 ga watan Agusta, tare da shugaban APC na kasa, Abdullahi Ganduje
- Ganduje ya bada tabbacin cewa a gwamnatinsa za a ga yan jam'iyyun adawa suna ta shigowa APC kafin babban zaben 2027
Gidan Gwamnati, Abuja - Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma da daya cikin magabatansa, a halin yanzu suna taro da Shugaban Kasa, Asiwaju Bola Tinubu, a fadar shugaban kasa a ranar Alhamis, 17 ga watan Agusta.
Uzodinma, Okorocha sun ziyarci Tinubu a Villa
Uzodinma da Okorocha, wanda sun dade suna rikici a shekarun baya sun isa fadar shugaban kasar ne a ranar Alhamis 17 ga watan Agusta tare da shugaban jam'iyya na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, The Nation ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Amma, bayan yan mintuna kimanin biyar, an hangi mutanen uku sun fito tare da gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu.
Ganduje, Sanwo-Olu sun raka Uzodinma da Okorocha su gana da Tinubu
Amma, an tattaro cewa shugaban kasar ya riga ya bar ofishinsa kafin su iso.
Mutanen uku - Ganduje, Uzodimma da Okorocha kuma sun tafi ofishin mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima.
Wani majiya daga fadar shugaban kasa ta ce akwai yiwuwar Ganduje ya kai Uzodimma da tsohon dan jam'iyyarsu da ake kai ruwa rana da shi Okorocha da Gwamna Sanwo-Olu gidan shugaban kasa.
Duk da cewa ba a san dalilin taron ba a lokacin hada wannan rahoton, ba zai rasa nasaba da rikicin da ke tsakanin Uzodinma da Okorocha ba wanda ya mulki jihar Imo tsakanin shekarar 2011 da 2019.
Dakaci karin bayani ...
Asali: Legit.ng