Kano: "APC Za Ta Fatattaki Abba Gida Da Sauransu a Kotu", Abdullahi Abbas
- Jam'iyyar APC a jihar Kano ta nuna kwarin gwiwar cewa za ta kwato karin kujeru a kotun zabe
- Abdullahi Abbas, shugaban APC a jihar ya ce daga cikin kujerun da za su kwato harda na Gwamna Abba Kabir Yusuf
- A ranar Alhamis ne kotun zabe ta sauke dan majalisa mai wakiltan mazabar tarauni wanda ya kasance dan NNPP daga kujerarsa
Jihar Kano - Shugaban jam'iyyar All Progressives Congress a jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas, ya bayyana cewa jam'iyyar za ta kwato karin kujeru a kotun zabe, ciki harda kujerar gwamna Abba Kabir Yusuf.
Jaridar Punch ta rahoto cewa Abbas ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, yayin da yake martani ga hukuncin da kotun zabe ta yanke a baya-bayan nan.
Ya ce yawancin yan takarar da suka yi ikirarin sun lashe zabe a karkashin inuwar jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPC) a jihar basu ci zaben ba.
Rundunar Tsaro Ta Yi Kakkausar Suka Ga Masu Tunzura Ta Don Kifar Da Gwamnatin Tinubu, Ta Fadi Matsayarta
A ranar Alhamis ne kotun zaben majalisar dokoki na kasa da jiha ta tsige mamba mai wakiltan mazabar Tarauni a majalisar wakilai, Umar Yerima, saboda kirkirar takardar shaidar kammala karatu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
An zabi Yerima a majalisar wakilai karkashin inuwar jam'iyyar NNPP.
Kotu za ta kwace kujerun ta mika su ga wadanda suka cancanta, Abbas
Sai dai kuma Abbas, ya yi zargin cewa kimanin mambobin majalisar wakilai biyar na jam'iyyar NNPP suna fuskantar shari'a na gabatar da takardun bogi.
Abbas ya kara da cewar:
"Muna da yakinin cewa a karshensa, karin kujeru za su dawo hannun APC a kotun. Wannan somin tabi ne. Hatta ga kujerar gwamna zai dawo garemu a karshe. Sun keta ka’idoji da dama da suka shafi gudanar da zabuka a lokacin zabe, don haka za a mayar da kujerun ga wadanda suka cancanta."
Kotun zabe ta tsige dan majalisa na NNPP daga kujerarsa a Kano
A wani labarin kuma, Legit.ng ta rahoto a baya cewa majalisar dokoki na kasa da jiha wacce ke zama a Kano ta soke zaben mamba mai wakiltan mazabar Tarauni a majalisar dokokin tarayya, Mukhtar Yarima.
Kotu ta fatattaki Yarima wanda ya kasance dan jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) kan zargin kirkirar takardar karatu na bogi.
Asali: Legit.ng