Gwamnan Arewa Ya Amsa Kira, Ya Bai Wa Dan Ibo Babban Mukami a Gwamnatinsa

Gwamnan Arewa Ya Amsa Kira, Ya Bai Wa Dan Ibo Babban Mukami a Gwamnatinsa

  • Gwamna Mohammed Bago na Neja ya amsa kiran da kungiyar Ibo mazauna jiharsa suka yi masa
  • Bago ya baiwa Mista George Dike wanda ya kasance dan kabilar ibo mukamin mai ba shi shawara na musamman kan harkokin kabilu
  • Gwamnan ya kuma nada wasu hadimai 25 a mukamai daban-daban a gwamnatinsa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Neja - Yan kwanaki bayan yan kabilar Ibo mazauna jihar Neja sun bukaci a basu gurbi a majalisar Gwamna Mohammed Bago, gwamnan ya nada Mista George Dike a matsayin mai ba shi shawara na musamman kan harkokin kabilu.

Gwamnan ya kuma nada wasu mutum 25 a matsayin masu ba shi shawara na musamman a bangarori daban-daban. Sunayen ya kunshi mata da maza daga jihar, rahoton Punch.

Umaru Mohammed Bago ya ba dan Ibo mukami
Gwamnan Arewa Ya Amsa Kira, Ya Baiwa Dan Igbo Babban Mukami a Gwamnatinsa Hoto: Umaru Mohammed Bago
Asali: Facebook

Babban sakataren labaran gwamnan, Bologi Ibrahim, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya saki a yammacin ranar Litinin, 8 ga watan Yuli.

Kara karanta wannan

"Yaron Na Daban Ne" Mahaifin Isa, Yaron Da Ya Zama Kwaro A WAEC Ya Fadi Yadda Ya Taimaki Dan Nasa, Ya Ce Yasan Zai Iya

Yanzu jimillar masu bayar da shawara na musamman ya zama 30 a karkashin gwamnatin Bago.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mun dai ji tun da farko cewa Al'ummar Igbo mazauna jihar Neja sun yi kira ga Gwamna Mohammed Bago da ya nada daya daga cikinsu a majalisarsa saboda gudunmawar da suke bayarwa wajen tattara kudaden shiga a jihar.

Yayin da yake taya su murna, gwamnan ya ce an nada su ne biyo bayan nasarorin da suka samu, rahoton Daily Post.

Bago ya yi kira garesu da su jajirce sannan su shayar da jihar tarin kwarewarsu don ci gaba da bunkasar jihar.

Jerin sunayen sauran mutane 25 da Bago ya ba mukami a gwamnatinsa

Mohammed Kolo (Harkokin siyasa), Mohammed Mariga, (Harkokin majalisa), Barista Manko Bagudu (Al'amuran Shari'a/lauyan Gidan Gwamnati), Mohammed Nda (Harkokin tattalin arziki).

Sai Isah Audu (Harkokin jama'a), Adam Erena (Harkokin kwadago), Dr. Isah Adamu (Shugabanci da sauye-sauye), Hon. Abdulmalik Dakachi, (Majalisun gargajiya).

Kara karanta wannan

Jarumin Gwamna Ya Jagoranci Jami’an Tsaro An Dura Gungun ‘Yan ta’adda Cikin Dare

Kabiru Abbas (Ayyuka da sanya ido), Umar Abubakar, (Manufofi da Dabaru), Yusuf Kolo (Manyan Laifuka da Cin zarafi), Alqassim Abdulkhadir, (Harkokin Gwamnati), Hauwa Mohammed (Shirin Zuba Jari ), Ndajiya Nma (Ma'adinai/Bida Basin), Habila Daniel (Al'amuran Muhalli).

Har ila yau, a jerin hadiman akwai Mary Noel-Berje (Harkokin mata), Ibrahim Panti (shirin raya gudunma), Hannatu Salihu shirin ilimin yara mata), Jonathan Vatsa (Hadin gwiwar gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu), Baba Ndaman (Manufofin ci gaba).

Sauran sune Mohammed Wakili (Harkokin tsaro), Abdullahi Suleiman (ci gaban wasanni), Dr. Mahmud Mamman (Tsare-tsare da kididdiga), Tsalha Buhari (Harkokin tsafta) da Remi Makun (CSR).

Legit.ng ta zanta da wasu Ibo mazauna garin Minna don jin yadda suka ji a lokacin da gwamna ya nada dan uwansu a matsayin hadiminsa.

Chimma Okereke ta bayyana cewa ta ji dadin wannan al’amari matuka domin a cewarta hakan ya nuna ana yi da su.

Ta ce:

Kara karanta wannan

Ku Yi Hakuri: Shugabannin 'Yan Bindiga a Arewa Sun Nemi Afuwa, Za Su Ajiye Makamai

“Gaskiya Gwamna Bago ya yi mana karamci, ya nuna muma yan kasa ne. Kamar ni yanzu Minna ne garina a cikinta aka haifeni, a cikinta na taso, yanzu ba dayanmu mukami da aka yi zai kara tabbatar mana da cewar ana yi da mu.”

A nasa bangaren, Okoye Anselm ya nuna godiyarsa a kan wannan abu da Gwamna Bago ya yi. Ya kuma ce za su ci gaba da marawa gwamnatinsa baya.

Ya ce:

“Muna mika godiyarmu ga mai girma Gwamna Mohammed Umar Bago bisa nada dan uwanmu da ya yi a matsayin hadiminsa, Allah ya saka da alkhairi. Za kuma mu ci gaba da ba gwamnatinsa goyon baya dari bisa dari.”

Majalisar dattawa ta nada shugabannin kwamitoci

A wani labarin, mun ji cewa Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya sanar da shugabannin kwamitocin majalisar dattawan a ranar Litinin, 7 ga watan Agusta.

Shugaban majalisar dattawan ya bayyana shugabannin kwamitocin majalisar bayan tabbatar da 45 daga cikin ministocin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu 48 a zaman majalisar na ranar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng