Buhari Ya Fadi Dalilin Ƙin Halartar Taron da Ganduje Ya Zama Sabon Shugaban APC
- A makon nan ne Shugabannin jam’iyyar APC su ka yi zaman Majalisar koli (NEC) a birnin Abuja
- Jam’iyyar APC ta aikawa Muhammadu Buhari goron gayyata, amma ba a gan shi a wajen taron ba
- Garba Shehu a wani jawabi da ya fitar, ya fadi abin da ya hana Buhari samun halartar zaman
Abuja - Shugabannin jam’iyyar APC na kasa sun yi taron majalisar koli watau NEC a ranar Alhamis, 3 ga watan Agusta 2023, a birnin tarayya Abuja.
Ko da aka laluba, sai aka lura Muhammadu Buhari bai samu halartar zaman ba, tashar Arise ta rahoto tsohon shugaban Najeriyan ya bada uzuri.
A wani bayani da ya yi ta bakin Garba Shehu, tsohon shugaban kasar ya ce bai samu zuwa wajen taron ba ne domin ya yi alkawarin wasu abubuwan.
Mai magana da yawun shugaban yake cewa yana fatan ayi taron lafiya, kuma a kammala lafiya. Malam Shehu ya fitar da jawabin a shafinsa.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Jawabin Garba Shehu
"Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi bayanin dalilin gazawarsa wajen zuwa zaman shugabannin APC da na majalisar koli da duk sauran taron da aka gayyace shi.
Ya aika da afuwarsa, ya nuna bai iya halarta ba ne saboda alkawuran da ya dauka a baya.
Tsohon shugaban Najeriyan ya yi amfani da damar wajen nuna goyon bayansa da jajircewa ga jam’iyyar.
Sannan ya na mai fatan ayi taro lafiya, a dauki muhimman matakan da su ka shafi jam’iyya da kasar.”
- Garba Shehu
Ba a ga keyar Buhari da Osinbajo ba
Daily Trust ta ce Mai girma Muhammadu Buhari ya bi sahun mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo wanda shi ma bai taka kafarsa zuwa wajen taron ba.
Tsohon mataimakin shugaban Najeriyan ya bada uzuri ne da cewa ya na wajen kasar nan.
An samu canji a APC NWC
Rahoton da aka samu ya ce Babban mai ba jam’iyyar APC shawara a kan harkar shari’a, Ahmad El-Marzuq ya yi murabus, ya fice daga majalisar NWC.
A wajen zaman na yau ne Abdullahi Umar Ganduje ya tabbata a matsayin sabon shugaban APC na kasa, Basiru Ajibola ya zama Sakataren jam’iyya.
Asali: Legit.ng