Cire Tallafin Mai: Najeriya Na Farin Cikin da Mulkinka, APC Ga Shugaba Tinubu

Cire Tallafin Mai: Najeriya Na Farin Cikin da Mulkinka, APC Ga Shugaba Tinubu

  • Jam'iyyar APC ta faɗa wa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu cewa Najeriya na farin ciki da kamun ludayinsa cikin wata biyu
  • Muƙaddashin shugaban APC na ƙasa, Abubakar Kyari ne ya faɗi haka a wurin taron NEC, inda aka zabi Ganduje a matsayin shugaba
  • Ya kuma taya ɗaukacin mambobin APC murna bisa nasarar da jam'iyyar ta samu a babban zaɓen 2023 da ya gabata

FCT Abuja - Shugabannin jam’iyyar APC mai mulki sun shaida wa shugaban kasa, Bola Tinubu cewa Najeriya tana farin ciki da shi bisa jajircewa da matakan da ya ɗauka zuwa yanzu.

Da zuwan shugaban Tinubu kan madafun iko ya dakatar da biyan kuɗin tallafin man fetur sannan kuma ya tsame hannun gwamnati daga harkokin musayar kuɗi, da sauran matakai da dama da ya ɗauka.

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
Cire Tallafin Mai: Najeriya Na Farin Cikin da Mulkinka, APC Ga Shugaba Tinubu Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

‘Yan Najeriya da dama sun koka kan yadda ake fama da wahalhalu sakamakon tashin farashin man fetur, amma shugaban kasar ya tabbatar wa da jama’a cewa wahalar ta wucin gadi ce.

Kara karanta wannan

Cire Tallafi: "Ko Kobo Ba'a Ceto Ba" NLC Ta Maida Martani Mai Zafi Kan Kalaman Shugaba Tinubu

Da yake jawabi a ranar Alhamis a taron majalisar zartarwa ta kasa karo na 12 na jam’iyyar APC, muƙaddashin shugaba na kasa, Abubakar Kyari, ya yaba da matakan da Tinubu ya dauka.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Najeriya tana cikin farin ciki da mulkinka bisa jajircewa wajen ɗaukar matakai masu tsauri," Kyari ya faɗa wa Tinubu a jawabinsa na maraba.

A rahoton Daily Trust, ya kara da cewa manufofin da gwamnatin Tinubu ta aiwatar a cikin watanni biyun da suka gabata sun kafa ginshikin ci gaba da bunƙasar Najeriya.

Kyari ya taya zababbun shugabanni murnar lashe zaɓe

Kyari, wanda kwanan nan aka zabe shi a matsayin minista, ya taya shugaban kasa, mataimakin shugaban kasa da daukacin zababbun APC murnar nasarar da suka samu a zaben.

Ya yi alkawarin cewa jam’iyyar APC za ta ci gaba da kasancewa tare da Shugaba Tinubu, “komai sarkakiyar kalubalen da zai iya fuskanta a gaba."

Kara karanta wannan

Bayan Taro a Aso Villa, NLC Ta Yi Magana Kan Janye Zanga-Zanga da Shiga Yajin Aikin da Ta Shirya a Najeriya

Ya ce jam’iyya mai mulki tana sane da sabbin kalubalen da ke gabanta a matsayinta na jam’iyya mai rinjaye a matakin jiha da kuma majalisar dokoki ta kasa.

The Nation ta rahoto cewa a wurin wannan taro ne, aka zabi tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje a matsayin sabon shugaban APC na ƙasa.

Fani-Kayode Ya Yi Magana Bayan Rashin Ganin Sunansa a Ministoci, Ya Fadi Mataki Na Gaba

A wani labarin kuma Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, ya bayyana ministocin da shugaba Tiɓubu ya naɗa a matsayin nagartaccen zaɓi.

Haka zalika, tsohon ministan kwadago, Festus Keyamo, ya ce ya ji dadin jerin sunayen ministoci na biyu da shugaba Tinubu ya tura majalisar dattawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262