Abdullahi Ganduje: Jerin Shugabannin APC Na Kasa Da Suka Fito Daga Arewacin Najeriya
FCT, Abuja - Majalisar zartaswa ta ƙasa (NEC) ta jam'iyyar All Progressives Congress (APC), a ranar Alhamis, 3 ga watan Agusta, ta zaɓi Abdullahi Umar Ganduje a matsayin sabon shugaban jam'iyyar na ƙasa.
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Kamar yadda The Nation ta rahoto, Shugaba Bola Ahmed Tinubu da jiga-jigan jam'iyyar APC sun halarci taron majalisar zartaswar na jam'iyyar karo na 12.
Abdullahi Ganduje shi ne shugaban jam'iyyar APC na ƙasa na huɗu da ya fito daga Arewacin Najeriya. Hakan na nufin Ganduje wanda na hannun daman Shugaba Tinubu ne, ya karɓi ragamar shugabancin jam'iyyar daga Abubakar Kyari.
Vanguard ta rahoto zaman Ganduje a matsayin sabon shugaban jam'iyyar APC. Kyari ya maye gurbin Sanata Abdullahi Adamu ne bayan ya yi murabus a cikin watan Yuli.
Matawalle, El-Rufai Da Tsofaffin Gwamnonin 3 Da Sunayensu Ya Fito Cikin Ministocin Tinubu Kashi Na Biyu
Tun lokacin da ƴan Kudancin Najeriya uku (Bisi Akande, John Oyegun, da Adams Oshiomhole) suka riƙe shugabancin APC a jere tun daga shekarar 2013 lokacin da aka kafa ta, Arewacin Najeriya ya samar da shugabanni sau huɗu.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
1) Mai Mala Buni (2020-2022)
Mai Mala Buni shi ne kan kujerar shugabancin jihar Yobe tun daga shekarar 2019 har zuwa yanzu.
Mai Mala Buni ya riƙe shugabancin jam'iyyar APC lokacin yana kan kujerar gwamnan jihar Yobe. Kafin zamansa gwamna ya taɓa riƙe sakataren jam'iyyar na ƙasa.
2) Abdullahi Adamu (2022 - 2023)
Abdullahi Adamu shi ne gwamnan jihar Nasarawa daga 29 ga watan Mayun 1999, zuwa 29 ga watan Mayun 2007.
A watan Maris na shekarar 2022, Abdullahi Adamu ya zama shugaban jam'iyyar APC na ƙasa. Ya yi murabus a ranar Lahadi, 16 ga watan Yulin 2023.
3) Abubakar Kyari (Yuli 2023 zuwa Agusta 2023)
Kyari shi ne sanatan Borno ta Arewa a majalisar dattawa ta tara tun daga shekarar 2015 har zuwa watan Afirilun 2022 lokacin da ya yi murabus.
Kyari mai shekara 60 a duniya shi ne muƙaddashin shugaban jam'iyyar APC na ƙasa.
4) Abdullahi Ganduje (Agusta 2023 zuwa abinda ya samu)
Ganduje ya riƙe gwamnan jihar Kano daga shekarar 2015 zuwa shekarar 2023.
Ya taɓa riƙe muƙamin mataimakin gwamna har sau biyu a gwamnatin Rabiu Musa Kwankwaso daga shekarar 1999 zuwa 2003, sannan daga shekarar 2011 zuwa shekarar 2015.
Bayan an daɗe ana raɗe-raɗin zamansa shugaban APC na ƙasa, Ganduje ya zama shugaban jam'iyyar a ranar 3 ga watan Agustan 2023.
Shugaba a APC Ya Yi Murabus
A wani labarin kuma, babban mai ba jam'iyyar All Progressives Congress (APC) sjawara kan harkar shari'a, ya yi murabus daga muƙaminsa.
Ahmad El-Marzuk ya gabatar da takardarsa ta murabus daga jam'iyyar APC ne a ranar Laraba, 2 ga watan Agustan 2023.
Asali: Legit.ng