Jerin Sunayen Ministoci 14 da Majalisar Dattawa Ta Tantance Kawo Yanzu

Jerin Sunayen Ministoci 14 da Majalisar Dattawa Ta Tantance Kawo Yanzu

A ranar Litinin, 31 ga watan Yuli, 2023 majalisar dattawan Najeriya ta fara zaman tantance rukunin farko na ministoci 28 waɗanda shugaban ƙasa ya aike mata.

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

A ranar farko, majalisar dattawa ta samu damar tantance mutum 14 daga cikin sunayen mutum 28 da Bola Tinubu ya naɗa a matsayin ministoci, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Zauren majalisar dattawa.
Jerin Sunayen Ministoci 13 da Majalisar Dattawa Ta Tantance Kawo Yanzu Hoto: NGRSenate
Asali: Facebook

Bayanai sun nuna cewa duk ministan da ya kasance tsohon sanata ne, majalisar ba ta tsitsiye shi da tambayoyi ba, ta umarci ya risina kawai ya kama gabansa.

Sai dai sauran waɗanda ba Sanatoci bane sun fuskanci tambayoyi daga wurin Sanatoci yayin tantance su. Amma tsohon gwamnan Ribas, Nyesom Wike bai sha walala ba.

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya bayyana cewa sun umarci Wike ya risina ya wuce ne saboda ya taɓa riƙe minista kuma majalisa ta taba tantance shi.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Majalisa Ta Tantance Mutum 20 Cikin Wadanda Tinubu Ke Son Nadawa Minista, Bayanai Sun Fito

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jerin sunayen waɗanda majalisa ta tantance a jiya Litinin

Legit.ng Hausa ta tattaro muku jerin sunayen ministocin da suka tsallake matakin tantancewa a majalisar dattawa da jihohinsu, ga su kamar haka;

1. Nyeson Wike (Ribas)

2. Abubakar Kyari (Borno)

3. Nkiruka Onyejeocha (Abia)

4. Bello Muhammad (Sakkwato)

5. Sani Abubakar Danladi (Taraba)

6. Muhammad Badaru Abubakar (Jigawa)

7. Joseph Utsev (Benue)

8. Olubunmi Tunji Ojo (Ondo)

9. Betta Edu (Cross River)

10. Uju Kennedy Ohaneye (Anambra)

11. John Enoh (Cross River)

12. Iman Suleiman Ibrahim (Nasarawa)

13. Yusuf Maitama Tuggar (Bauchi)

14. Abubakar Momoh (Edo)

Majalisa ta ɗage zaman

Bayan kammala tantance su, shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa, Sanata Opeyemi Bamidele, ya gabatar da kudirin majalisa ta koma ainihin zamanta domin duba ci gaban da aka samu.

Nan take shugaban marasa rinjaye, Sanata Darlington Nwokocha, ya goyi bayan kudirin kuma aka aiwatar duk a jiya Litinin.

Kara karanta wannan

Ministocin Tinubu: Babban Dalilin da Ya Sa Majalisar Dattawa Ba Ta Tsitsiye Wike Ba Ya Bayyana

Bayan nan ne, Sanata Godswill Akpabio ya ɗaga zaman zuwa washe gari ranar Talata, 1 ga watan Agusta, 2023, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Shugaba Tinubu Ya Sanar da Sabuwar Garaɓasa Ga Ɗaliban Najeriya

A wani rahoton na daban kuma Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da raba wa manyan makarantun gaba da sakandire motocin zirga-zirgar ɗalibai.

Sanarwan ta ce shugaba Tinubu ya bada umarnin raba motocin Bas-Bas ga jami'o'i, kwalejojin fasa da kwalin ilimin da ke sassan ƙasar nan baki ɗaya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262