Shugaba Bola Tinubu Ya Nada Tsohon Hadimin Osinbajo a Matsayin Kakakinsa

Shugaba Bola Tinubu Ya Nada Tsohon Hadimin Osinbajo a Matsayin Kakakinsa

  • Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya naɗa sabon mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin midiya da yaɗa labarai
  • Tinubu ya naɗa Ajuri Ngelale, tsohon hadimin tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Yemi Osinbajo a matsayin kakakinsa
  • Mista Ngelale ya yaba da abinda ya kira karamcin shugaba Tinubu, inda ya sha alawashin zai yi iya bakin kokarinsa

FCT Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da nadin Ajuri Ngelale a matsayin mai bai wa shugaban kasa shawara ta musamman kan harkokin midiya da yada labarai.

Mista Ngelale ya kasance babban mataimaki na musamman kan harkokin al'umma a fadar shugaban kasa a tsohuwar gwamnatin da ta shude karkashin Muhammadu Buhari.

Shugaba Tinubu da sabon mai magana da yawunsa.
Shugaba Bola Tinubu Ya Nada Tsohon Hadimin Osinbajo a Matsayin Kakakinsa Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Ajuri Ngelale
Asali: Facebook

Haka zalika a wancan lokaci, ya yi aiki ne a ofishin tsohon mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: "Mun Tara Sama da N1tr" Shugaba Tinubu Ya Tona Kuɗin Da Ya Ƙwato Bayan Cire Tallafin Fetur

Daraktan yaɗa labarai na ofishin sakataren gwamnatin tarayya, Willie Bassey, shi ne ya sanar da wannan saɓon naɗin da shugaba Tinubu ya yi ranar Litinin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce naɗin zai fara aiki ne daga yau Litinin 31 ga watan Yuli, 2023 kuma zai karkare a karshen wa'adin gwamnati mai ci sai dai kuma idan shugaban kasa ya canza shawara.

Sanarwar ta ce "Shugaban ƙasa ya bukace shi da ya baje kolin kwarewarsa domin tafiyar da sabon ofishinsa."

Mista Ngelale, shi ne mataimakin babban kakakin kwamitin yaƙin neman zaben shugaban ƙasa na jam’iyyar APC (PCC) a zaben 2023 da ya gabata.

Sabon kakakin shugaban ƙasa ya yi magana

Ajuri Ngelale ya tabbatar da naɗa shi a matsayin mai magana da yawun shugaban ƙasa a shafinsa na Tuwita. Ya yaba wa Tinubu bisa ganin ya dace

Kara karanta wannan

Mu je zuwa: Tinubu ya nada fitaccen masani don yin bincike a lamurran CBN

Sabon hadimin shugaban ƙasan ya ce ya yi farin cikin bisa wannan karrama w ada shugaban ƙasa Tinubu ya masa na ganin ya dace ya zo ya sake bada gudummuwarsa.

"Zan yi iya bakin kokarina kamar yadda na saba," inji shi.

Mun Tara Sama da Tiriliyan N1tr Daga Cire Tallafin Man Fetur, Shugaba Tinubu

A wani rahoton kuma Shugaba Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinaa ta tattala naira tiriliyan ɗaya daga lokacin cire tallafin mai zuwa yanzu.

Tinubu ya ce duk waɗan nan kuɗaɗe wasu yan tsirarun mutanene suke amfana da su amma yanzu za a karkatar da su zuwa yan Najeriya kai tsaye.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262