Majalisar Dattawa Ta Tantance Ministan Shugaba Tinubu da Ya Fara Karatu Yana Shekara 3

Majalisar Dattawa Ta Tantance Ministan Shugaba Tinubu da Ya Fara Karatu Yana Shekara 3

  • Ministan da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya naɗa daga jihar Benuwai ya haddasa ruɗani da kace-nace a majalisar dattawa
  • Yayin tantance shi ranar Litinin, Farfesa Utsev ya faɗa wa majalisa cewa an haife shi a 1980 kuma ya fara karatun Firamare a 1984
  • Wannan batu dai ya haddasa cece-kuce tsakanin Sanatoci amma daga karshe an umarci ya risina wa majalisa ya ƙara gaba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT Abuja - Ɗaya daga cikin ministocin da shugaba Bola Tinubu ya naɗa, Farfesa Joseph Utsev, ya haddasa ruɗani da cece-kuce a majalisar dattawa kan shekarun da ya fara makarantar firamare.

Takardar da ke ƙunshe da bayanan karatun Farfesa Utsev (CV) ta nuna cewa ya fara makarantar firamare tun yana dan shekara uku a duniya, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ministocin Tinubu: Babban Dalilin da Ya Sa Majalisar Dattawa Ba Ta Tsitsiye Wike Ba Ya Bayyana

Majalisar dattawa na ci gaba da tantance ministoci.
Majalisar Dattawa Ta Tantance Ministan Shugaba Tinubu da Ya Fara Karatu Yana Shekara 3 Hoto: NGRSenate
Asali: Facebook

Sanata Mikhail Abiru (APC, Legas) shi ne ya ja hankalin abokan aikinsa kan CV ɗin Ministan, wanda ya bayyana ƙarara cewa an haifi Farfesa Utsev a shekarar 1980

Haka zalika CVn ministan ya nuna cewa ya shiga makarantar Firamare a shekarar 1984 kuma ya kammala karatun Firamare a 1989.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yadda Sanatoci suka yi cece kuce kan batun shekarun karatun ministan

Sanata Abiru ya bukaci wanda ake shirin naɗa wa Minista ya fayyace ranakun da ya fara karatunsa, inda ya ce da alama akwai rudani a tarihin karatunsa.

Da yake ba shi amsa, Farfesan ya jaddada cewa an haife shi a 1980 kuma ya kammala karatunsa na farko da shaidar kammala karatun Firamare a shekarar 1989.

Sanata Abba Moro (PDP, Benue) ya roki Sanatoci su yi watsi da ruɗanin shekarun karatunsa, yana mai cewa ta yiwu hakan ya faru ne sakamakon kuskuren rubutu.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Taƙaddama Ta Barke a Majalisar Dattawa Yayin Tantance Wani Minista Daga Arewa

"Idan muka yi la'akari da takardar bayanan karatun Farfesa Utsev, babu wani abun saɓani saboda mai yuwuwa kuskuren rubutu ne. Ya kamata mu daina shakku."

Sai dai Titus Zam, Sanata daga Benue, ya ki amincewa da batun Moro, yana mai cewa babu wani sabani a cikin bayanan karatun ministan.

Wane mataki majalisa ta ɗauka kan ministan?

Bayan sauraron bayanan sanatocin da cece kucen da ya biyo baya, shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya kulle tambayoyin da suka shafi bayanan karatun ministan.

Akpabio ya ce:

"Ba zan sake sauraron komai ba kan batun lokacin da ya shiga makaranta. Sanata Abba Moro ya ja hankali na ga wani muhimmin al’amari wanda ministan ne kaɗai zai fayyace"

Daga nan sai majalisar ta umarci Farfesan ya risina ya kama gabansa bayan ya yi bayani kan yadda zai tafiyar da ɓangaren muhalli a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262