Takaddama Ta Barke a Majalisa Kan Shekarun Ministan Shugaba Tinubu

Takaddama Ta Barke a Majalisa Kan Shekarun Ministan Shugaba Tinubu

  • A ranar Litinin ɗin nan, 31 ga watan Yuli, 2023, majalisar dattawa ta fara aikin tantance mutanen da shugaban ƙasa ya naɗa ministoci
  • Rahoto ya nuna a lokacin da aka zo kan Farfesa Joseph Turlumum an samu hatsaniya kan shekarun karatunsa
  • Makon da ya gabata, shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tura sunayen ministoci 28 ga majalisar ta hannun shugaban ma'aikatan Villa

FCT Abuja - Taƙaddama ta ɓarke a majlisar dattawan Najeriya kan bayanan shekarun Farfesa Joseph Turlumum, ɗaya daga cikin ministocin da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya naɗa.

A zaman tantancewa da Sanatocin suka fara yau Litinin, an tada jijiyoyin wuya game da bayanan shekarun Farfesa Turlumum da na karatunsa a daidai lokacin da ake tantance shi a matsayin Minista.

Zauren majalisar dattawan Najeriya.
Takaddama Ta Barke a Majalisa Kan Shekarun Ministan Shugaba Tinubu Hoto: SenateNGR
Asali: Facebook

Majalisar dattawa ta ƙasa ta fara aikin tantance jerin sunayen ministocin da shugaba Tinubu ya aika mata a ranar Alhamis, 27 ga watan Yuli, 2023, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Bayan Cece-Kuce, Majalisar Dattawa Ta Ɗauki Matsaya Kan Ministan da Ya Fara Firamare Yana Shekara 3

Sai dai lokacin da aka zo kan Farfesa Turlumum, taƙaddama mai zafi ta ɓarke tsakanin mambobin majalsar kan bayanan shekarunsa da na shekarun karatunsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

BBC Hausa ta tattaro wa Farfesa Farfesa Joseph Turlumum ɗan asalin jihar Benuwai ne da ke shiyyar Arewa ta Tsakiya a Najeriya.

Yadda majalisar ta fara tantance ministocin Bola Tinubu

Mutum na farko da ya fara bayyana a gaban Sanatocin domin tantance shi kuma na farko a jerin sunayen da shugaban ƙasa ya tura shi ne Abubakar Momoh ɗan asalin jihar Edo.

Amma kasancewarsa tsohon ɗan majalisar wakilan tarayya, Mista Mamoh bai fuskanci turjiya da rubdugun tambayoyin daga sanatocin majalisa ta 10 ba.

Ba tare da ɗaukar dogon lokaci ba, shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya umarci Mista Abubakar Momoh ya risina wa sandar majalisa ya ƙara gaba.

Kara karanta wannan

Fadar Shugaban Ƙasa Ta Bai Wa Ministoci 28 Sabon Umarni, Sun Shiga Mataki Na Gaba

Har kawo yanzu ba bu wani cikakken bayani kan adadin waɗanda majalisar zata tantance daga cikin jerin sunayen ministocin a zamanta na yau Litinin, 31 ga watan Yuli.

Matasan APC da Mata Sun Roki Tinubu Ya Zabi Boss Mustapha a Matsayin Shugaban APC

A wani labarin na daban Matasa da matan jam'iyyar APC sun jingine Ganduje, sun roki shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya zaɓi wanda suke so ya shugabanci APC.

A cewarsu, a halin da APC ta tsinci kanta, tana bukayar gogaggun mutane da suka san harkar shugabanci kamar Mustapha.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel