Zaben Gwamnan Kogi: Yan Takara 5 Sun Janyewa Dan Takarar APC, Ododo

Zaben Gwamnan Kogi: Yan Takara 5 Sun Janyewa Dan Takarar APC, Ododo

  • A watan Nuwamba mai zuwa ne za a gudanar da zaben gwamna a jihar Kogi da ke arewa ta tsakiya
  • Jam'iyyar APC mai mulki ta kara samun karfi gabannin zaben inda yan takara biyar suka janyewa wanda ke rike da tutarta, Alhaji Ahmed Usman Ododo
  • Wadannan yan takara sune Omaji Sunday (APP), Prince Yahaya (ADP), Muhammed Kabir Umar (Boot Party), Bala Abdulghafar Idris (NRM) da Hon. Fatima Suleiman (ZLP)

Jihar Kogi - Rahotanni sun kawo cewa yan takarar kujerar gwamna biyar a zaben gwamnan jihar Kogi mai zuwa sun rushe tsarinsu.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto, wadannan yan takara sun kuma yanke shawarar goyon bayan dan takarar gwamna na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Alhaji Ahmed Usman Ododo.

Yan takarar gwamna biyar sun janyewa Ododo a jihar Kogi
Zaben Gwamnan Kogi: Yan Takara 5 Sun Janyewa Dan Takarar APC, Ododo Hoto: @KingsleyFanwo
Source: Twitter

An sanar da hakan ne a garin Lokoja, babban birnin jihar, jim kadan bayan ganawa da yan takarar gwamnonin da abun ya shafa.

Kara karanta wannan

Zababbun Ministocin Tinubu: PDP Ta Bayyana Lokacin Da Za Ta Yanke Hukunci Kan Makomar Wike

Wadannan yan takara biyar sun hada da Omaji Sunday na jam'iyyar APP, Prince Yahaya na ADP, Muhammed Kabir Umar na Boot Party, Bala Abdulghafar Idris na jam'iyyar NRM da Hon. Fatima Suleiman ta jam'iyyar ZLP, rahoton Independent.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilinmu na janyewa Ododo, yan takarar gwamnan Kogi 5

Yan takarar karkashin inuwar kungiyar 'United Progressive Political Parties' sun ce dalilinsu na janyewa Ahmed Usman Ododo don tabbatar da ci gaba da dorewar shirye-shiryen Gwamna Yahaya Bello ne.

Kakakin kungiyar, Bala Abdulghafar Idris, ya ce yan takarar sun yi mubaya'a da kafa Ahmed Ododo a matsayin babban direban gwamnati mai ci.

Ya ce:

“Kungiyar 'United Progressive Political Parties' ta duba cancantarsa, Karfi da iyawarsa. Alhaji Ahmed Usman Ododo iya shayar da mutane romon damokradiyya fiye da sauran yan takarar da ke tseren mukamin."

Hukumar DSS ta gayyaci dan takarar APC a zaben gwamnan jihar Kogi

A wani lamarin kuma, mun kawo a baya cewa Hukumar ƴan sandan farin kaya (DSS) ta gayyaci ɗan takarar gwamnan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Kogi, Ahmed Usman Ododo, domin amsa tambayoyi bayan wasu ƴan jam'iyyar adawa sun shigar da ƙorafi a kansa.

Kwamishinan watsa labarai da sadarwa na jihar Kogi, Kingsley Femi Fanwo, shi ne ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter, @KingsleyFanwo, a ranar Asabar, 29 ga watan Yuli.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng