Tsohon Bidiyon El-Rufai Da Ya Ce Ba Zai Karbi Muƙamin Minista Ba Ya Janyo Cece-Kuce

Tsohon Bidiyon El-Rufai Da Ya Ce Ba Zai Karbi Muƙamin Minista Ba Ya Janyo Cece-Kuce

  • An ga tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai na cewa ba zai amshi muƙamin minista ba
  • A cikin wani tsohon bidiyo da ya yaɗu a kafafen sada zumunta, an gan shi yana cewa ba adalci ba ne ya sake zama minista
  • El-Rufai dai ya yi wannan iƙirari ne a lokacin da ake shirye-shiryen zaɓen shekarar 2023

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wani tsohon bidiyo na tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya janyo zazzafar muhawara a kafafen sada zumunta.

A cikin bidiyon wanda wani mai suna Muhammed Auwal Muazu ya ɗora a shafinsa na Instagram, an ga El-Rufai na iƙirarin cewa ba adalci ba ne ya sake zama minista.

Tsohon bidiyon El-Rufai ya janyo cece-kuce
Ana tafka muhawara kan bidiyon El-Rufai da ya ce ba zai amshi muƙamin minista ba. Hoto: Nasir El-Rufai
Asali: Facebook

Na riƙe minista tun ina ɗan shekara 43, El-Rufai ya yi iƙirari

Malam Nasir El-Rufai a cikin bidiyon ya bayyana cewa tun yana ɗan shekara 43 ya riƙe muƙamin minista, don haka bai kamata a ce bayan shekara 20 ya dawo ya ce zai ƙara riƙe muƙamin ba.

Kara karanta wannan

Dalilin Da Ya Sanya 'Yan Bindiga Suka Kwamushe Ni, Babban Boka Ya Yi Bayani Bayan Ya Shaki Iskar 'Yanci

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce akwai ƙanne da 'ya'ya da ya kamata ace an ɓuɗawa hanya don suma su shiga a dama da su, ba wai mutum ɗaya yai ta riƙewa ba.

Ya ƙara da cewa ya riga da ya horar da mutane da dama da yake da tabbacin cewa za su iya riƙe kowane irin muƙami kuma su yi abinda ake so.

Martanin masu amfani da kafafen sada zumunta dangane da bidiyon na El-Rufai

Masu amfani da kafar Instagram da suka ci karo da wannan bidiyo na malam Nasir El-Rufai sun bayyana ra'ayoyi mabanbanta.

Hakan ya samo asali ne daga ganin sunan El-Rufai da aka yi, a cikin mutane 28 da Tinubu ya aika Majalisar Dattawa domin tantancesu dangane da muƙamin ministoci da zai ba su.

Ga wasu daga cikin ra'ayoyin masu amfani da kafar sada zumunta kan bidiyon na El-Rufai:

Kara karanta wannan

"Har Yanzu Yana Da Rai": Karamin Yaro Ya Tayar Da Gardama Mahaifinsa Bai Mutu Ba a Wajen Binne Gawa, Bidiyon Ya Sosa Zuciya

@ziter001 ya ce:

“Shi fa ɗan siyasa komai zai iya cewa. Ba za su iya rayuwa ba tare da gwamnati ba.”

@_aayshanagoda ta ce:

“Ya ce baya so daga farko shi ma da aka tambaye shi so don ya karɓa daga baya ai ba wani abu bane. Kila an sanya shi ya yarda ne. Kuma indai ya cancanta ai ba wani abu ba ne.”

@young_ustaax ya ce:

“Hakan nan gaba kadan za ayi ta dawo da bidiyoyinmu lokacin mu ne manyan ƙasar.”

@hajara_Is ta ce:

“Mun tattauna kan wannan bidiyon da 'yan uwana lokacin da aka bayyana sunayen ministocin. Shi fa zaƙin mulki daban yake, ba zan ga laifin kowa ba don ya yi irin waɗannan maganganu kuma in an ba shi ya karɓa.”
“A yi da kai ya fi a yi babu kai. Mu dai fatan mu Allah ya sa su zame mana alkhairi da abun alfahari.
“Baya ga haka, Malam jajirtacce ne, kuma ba zai ba mu kunya ba in sha Allahu.”

Kara karanta wannan

‘Ba Batun Neman Minista Ba Ne’, Jonathan Ya Bayyana Dalilin Kai Wa Tinubu Ziyara

@miss_sumee ta ce:

“Ba komai ya amsa abunshi yaran ba za su iya abinda zai yi ba, muna buƙatar mutane irinsa.”

Matasa da matan APC sun fadawa Tinubu wanda ya kamata ya zama shugaban jam'iyyar

Legit.ng ta yi wani rahoto a baya, kan bayanin da ƙungiyar matasa da mata na jam'iyyar APC suka yi wa Shugaba Tinubu, dangane da wanda ya kamata ya zama shugaban jam'iyyar.

Sun bayyana cewa tsohon sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha ne ya fi cancanta da ya zama shugaban jam'iyyar ta APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng