Ganduje Ka Iya Zama Shugaban APC Na Kasa a Taron NEC Ranar Alhamis
- Ga dukkan alamun za a naɗa tsohon gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Ganduje a matsayin shugaban jam'iyyar APC ranar Alhamis
- Ana tsammanin hakan zata faru ne a wurin taron majalisar zartarwa (NEC) wanda APC ta tsara gudanarwa ranar 3 ga watan Agusta
- Tuni shugaba Tinubu ya faɗa wa Ganduje shirinsa na maida shi shugaban APC don haka ya cire sunansa daga Ministoci
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT Abuja - A ranar Jumu'a (jiya) wasu alamu suka nuna cewa tsohon gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Ganduje, ka iya zama shugaban jam’iyyar APC na kasa a hukumance ranar Alhamis.
Leadership ta tattaro cewa da yuwuwar a naɗa Ganduje a matsayin shugaban APC a taron majalisar zartarwan jam'iyyar ta ƙasa (NEC) wanda zai gudana ranar Alhamis mai zuwa 3 ga watan Agusta, 2023.
Kwamitin ayyuka na jam’iyyar (NWC) ya tsara cewa taron NEC zai gudanar washe garin ranar taron shugabanni, wanda za a yi ranar Laraba, 2 ga watan Agusta.
Ganduje Ya Gamu da Cikas, Wasu Kusoshin APC Sun Faɗa Wa Tinubu Wanda Ya Cancanci Zama Shugaban APC Na Gaba
Tun fari APC ta tsara gudanar da waɗannan tarukan biyu a watan Yuli amma hakan bai yuwuwa ba sakamakon murabus ɗin tsohon shugaba, Abdullahi Adamu da sakatare, Iyiola Omisore.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ganduje ya samu goyon bayan shugaban ƙasa Tinubu
Sai dai an fahimci cewa duk da matsin lambar da aka yi wa shugaban ƙasa na ya bar kujerar shugaban APC a Arewa ta tsakiya, Bola Tinubu ya nuna Ganduje yake goyon baya.
Ana ganin cewa, "Ga dukkan alamu ya yi haka ne domin rarrashin shiyyar Arewa maso Yamma da ta dage sai ta samar da shugaban majalisar dattawa ta 10.”
Rahoto ya nuna gwamnonin APC hudu da suka hada da shugaban PGF kuma gwamnan Imo, Hope Uzodimma da takwaransa na jihar Kwara da wasu mutane biyu ne suka jagoranci Ganduje zuwa wurin Tinubu a Villa.
A wajen taron, shugaba Tinubu ya gaya wa tsohon gwamnan Kano shirin nada shi shugaban jam’iyyar APC na kasa, maimakon minista kamar yadda aka tsara tun farko.
Ya kuma bukaci Ganduje da ya kawo sunan wanda ya cancanta a naɗa shi a matsayin minista daga jihar Kano, kamar yadda Tribune ta rahoto.
Wasu Kusoshin APC Sun Faɗa Wa Tinubu Wanda Ya Cancanci Zama Shugaban APC Na Gaba
A wani labarin kuma Matasa da matan jam'iyyar APC sun jingine Ganduje, sun roki shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya zaɓi wanda suke so ya shugabanci jam'iyya.
A wani taron manema labarai a Kaduna, ƙungiyar matasa da matan ta ayyana goyon baya ga tsohon SGF, Boss Mustapha.
Asali: Legit.ng