Gwamna Zulum Ya Rantsar Da Wasu Masu Muhimman Mukamai a Gwamnatinsa
- Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno ya rantsar da sabon shugaban ma'aikatan jihar domin kama aiki gadan-gadan
- Farfesa Babagana Umara Zulum ya rantsar wasu sabbin masu ba shi shawara na musammnan a jihar ta Borno
- Gwamnan ya kuma rantsar da shugabannin riƙo na ƙananan hukumomi 27 dake a faɗin jihar domin fara aiki
Jihar Borno - Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum, ya rantsar da shugaban ma'aikatan jihar da wasu mutum biyu masu ba shi shawara na musamman.
Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa gwamnan ya kuma rantsar da shugabannin riƙon ƙwarya na ƙananan hukumomi 27 a jihar.
An gudanar da taron rantsar da sabbin masu muƙaman ne a ƙarƙashin jagorancin mataimakin gwamnan jihar, Umar Usman Kadafur, yayin da babban alƙalin alƙalai na jihar, mai shari'a Kashim Zannah, ya basu rantsuwar kama aiki.
Taron ya gudana ne ranar Juma'a, 28 ga watan Yuli a sakatariyar Musa Usman dake birnin Maiduguri, babban birnin jihar.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Waɗanda aka naɗa muƙaman sun haɗa da Malam Fannami wanda yake lauya ne a matsayin shugaban ma'aikatan jihar, Haruna Hassan Tela, a matsayin mataimakin shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin jihar.
Sauran sun haɗa da Isa Umar Gusau, a matsayin mai bayar da shawara na musamman kan watsa labarai da tsare-tsare da Birgediya Janar Abdullahi Ishaq, a matsayin mai bayar da shawara na musamman kan harkokin tsaro.
Dalilin ba su muƙaman da gwamna Zulum ya yi
Da yake jawabinsa a wajen taron, mataimakin gwamnan ya bayyana cewa naɗin da aka yi musu, an yi musu shi ne bisa cancanta, gaskiyarsu da kuma ƙwarewar da suka nuna a fannoninsu.
Ya buƙace su da su gudanar da ayyukansu ba tare da wani tsoro ba ko yi wa wani wata alfarma.
"Ana buƙatar ku gudanar da ayyukanku ba tare da jin tsoro ba ko nuna sanayya." A cewarsa.
Gwamna Zulum Ya Yi Sabbin Nade-Nade
A wani labarin kuma, gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya yi wasu sabbin naɗe-naɗe guda biyu masu muhimmanci.
Gwamna Zulum ya naɗa shugaban hukumae bayar da agajin gaggawa ta jihar (SEMA) da shugaban hukumar ilmin Larabci da tsangayu ta jihar (BOSASEB).
Asali: Legit.ng