Jam'iyyar APC Ta Sanya Ranakun Gudanar da Manyan Taruka Guda 2

Jam'iyyar APC Ta Sanya Ranakun Gudanar da Manyan Taruka Guda 2

  • Kwamitin gudanarwa na jam'iyyar APC ta ƙasa ya sanya ranakun gudanar da taron shugabanni da na majaliaar zartarwa (NEC)
  • Mukaddashin sakataren APC, Festus Fuater, ya sanar da cewa tarukan biyu zasu gudana a ranakun 2 da 3 ga watan Agusta, 2023
  • APC ta ɗage tarukan ne bayan murabus ɗin Sanata Abdullahi Adamu da Iyiola Omisore daga muƙamansu

Abuja - Kwamitin gudanarwa na jam'iyyar APC ta ƙasa (NWC) ya sanya ranar taron shugabanni masu riƙe da madafun iko da kuma taron majalisar koli (NEC).

Channels tv ta rahoto cewa kwamitin ya amince da ranar 2 ha watan Agusta a matsayin ranar taron shugabanni yayin da 3 ga watan Agusta, 2023 kuma za a yi taron NEC.

Mukaddashin shugaban APC na ƙasa, Abubakar Kyari.
Jam'iyyar APC Ta Sanya Ranakun Gudanar da Manyan Taruka Guda 2 Hoto: OfficialAPCNg
Asali: Twitter

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Juma’a a Abuja mai dauke da sa hannun mukaddashin sakataren jam’iyyar na kasa, Barista Festus Fuanter.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Wakilan Ƙungiyar Kwadugo NLC Sun Fice Daga Fadar Shugaban Kasa, Bayanai Sun Fito

Ya ce an fitar da sanarwar taron ne kamar yadda kundin tsarin mulkin jam’iyar APC ya tanada, inda ya kara da cewa wurin taron masu riƙe da muƙamai shi ne dakin taro na Banquet Hall na fadar shugaban kasa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Waɗanda ake tsammanin zasu halarci taron

Waɗanda ake tsammanin zasu halarci wannan taron sun ƙunshi, shugaban jam'iyya, mataimakansa na kudu da arewa, Sakatare, mai bada shawara kan shari'a, ma'ajiyi, sakataren tsare-tsare da shugabar mata.

Sauran sun haɗa da shugaban matasan APC, shugaban mutane masu buƙata ta musamman, tsoffin shugabannin ƙasa da mataimakansu, shugaban kasa mai ci da mataimakinsa da sauransu.

A gefe guda kuma, taron NEC wanda aka tsara a ranar 3 ga watan Agusta, an shirya gudanar da shi ne a otal din Transcorp Hilton da ke Abuja.

Tun da farko dai jam'iyya mai mulki ta sanya ranakun 18 da 19 ga watan Yuli domin gudanar da tarukan biyu, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Bayan Tsawon Lokaci, An Bayyana Sunan Sabon Shugaban Jam'iyyar APC a Jihar Arewa

Sai dai kuma bisa tilas aka dage tarukan biyu bayan murabus din da tsohon shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Adamu da sakatare, Iyiola Omisore suka yi a ranar 16 ga watan Yuli.

Wakilan Ƙungiyar Kwadugo NLC Sun Fice Daga Fadar Shugaban Kasa,

A wani labarin kuma Wakilan ƙungiyar kwadugo ta ƙasa (NLC) sun fice daga fadar shugaban ƙasa ba tare da an yi taro ba ranar Jumu'a.

FG na ci gaba da kokarin rarrashin NLC da ƙawayenta bayan sun yi barazanar shiga yajin aiki ranar 2 ga watan Agusta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262