Ministoci 28 da Tinubu Ya Nada Sun Shiga Mataki Na Gaba, An Fara Tantance Takardu

Ministoci 28 da Tinubu Ya Nada Sun Shiga Mataki Na Gaba, An Fara Tantance Takardu

  • Hadimin shugaban ƙasa, Sanata Abdullahi Gumel, ya ce sun fara tantance takardun waɗanda Bola Tinubu ya naɗa ministoci
  • Gumel ya buƙaci dukkan waɗanda sunansu ya shiga jerin ministocin su je ofishinsa daga nan zuwa ranar Lahadi
  • Ya ce suna fatan kammala tattara bayanan ministocin gabanin majalisar dattawa ta fara tantance su ranar Litinin

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT Abuja - Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa ta fara tantance takardun ministoci 28 da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya naɗa, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Babban mai taimaka wa shugaban kasa kan harkokin majalisar dattawa, Sanata Abdullahi Gumel ne ya faɗi haka yayin hira da yan jarida a Abuja ranar Jumu'a.

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
Ministoci 28 da Tinubu Ya Nada Sun Shiga Mataki Na Gaba, An Fara Tantance Takardu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Ya ce ana umartan dukkan ministocin su ziyarci ofishin hadimin Tinubu kan harkokin majalisa domin tantance takardun karatunsu daga ranar Jumu'a 28 zuwa Lahadi, 30 ga watan Yuli.

Kara karanta wannan

Jerin Sunaye: Gwamna Aliyu Ya Miƙa Sunayen Sabbin Kwamishinoni 16 Ga Majalisar Dokoki

Sanata Gumel ya yi bayanin cewa a wannan wa'adin na kwana 2 za a tantaɓce tare da karɓan takardun ministoci gabanin majalisa ta fara tantance su ranar Litinin 31 ga watan Yuli.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Mun fara tattara muhimman bayanai da takardun ministocin aka naɗa kuma ana tsammanin kowane minista ya kamma duk matakan da aka tsara kafin tantance shi a majalisa."
"Zamu buɗe ofis kan wannan batun ranar Jumu'a, Asabar da Lahadi, wannan zai ba mutanen da aka naɗa damar kammala matakin kai takardunsu kafin majalisa ta tantance su."

- Sanata Abdullahi Gumel.

Shugaba Tinubu ya miƙa sunayen ministoci ga majaliaar dattawa

Idan baku manta ba, a jiya Alhamis, 27 ga watan Yuli, 2023, shugaba Tinubu ya aike sunayen mutane 28 da ya naɗa a matsayin ministoci ga majalisar dattawa.

Shugaban majalisar, Sanata Godswill Akpabio, ya karanta sunayen bayan ya karɓa daga shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Magana Kan Ma'aikatun da Ministoci 28 Zasu Jagoranta

Fitaccen Gwamnan PDP Ya Yi Magana Kan Nada Wike a Matsayin Minista

A wani labarin na daban gwamna Fubara, ya taya magabacinsa, Nyesom Wike murnar shiga cikin jerin sunayen ministocin da shugaba Bola Tinubu ya nada.

Masana harkokin siyasa sun daɗe suna muhawara kan dalilin da ya sa shugaban ƙasa ya sanya Wike a cikin jerin ministocinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262