Majiyoyi Sun Bayyana Farfesan Likitanci, Pate Ali, a Matsayin Ministan Lafiyan Tinubu

Majiyoyi Sun Bayyana Farfesan Likitanci, Pate Ali, a Matsayin Ministan Lafiyan Tinubu

  • Wani sabon ci gaba ya yi ikirarin cewa an fallasa jerin sunayen ministocin Shugaban kasa Bola yayin da ake zaman jiran tsammani
  • Daya daga cikin sunayen da aka bankado a jerin ministocin Shugaban Kasa Tinubu shine Mohammed Ali Pate, tsohon karamin ministan lafiya
  • An tattaro cewa an zabi Pate domin ya zama sabon ministan lafiya a gwamnatin Tinubu

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Ana ta samun karin rade-radi dangane da jerin ministocin Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, wanda aka ce an aika majalisar dattawa don tabbatar da su.

Bayanai da ke fitowa daga wata majiya ta fadar Shugaban kasa ya bayyana cewa an saka sunan Muhammad Ali Pate, tsohon karamin ministan lafiya a gwamnatin tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan cikin jerin ministocin Shugaban kasa Tinubu.

Ana ganin Muhammad Pate ne zai zama ministan lafiya a gwamnatin Tinubu
Majiyoyi Sun Bayyana Farfesan Likitanci, Pate Ali, a Matsayin Ministan Lafiyan Tinubu Hoto: Bola Ahmed Tinubu/Muhammad Ali
Asali: Facebook

Kamar yadda jaridar The Nation ta rahoto, majiyar ta bayyana cewa an sanya sunan farfesan Likitancin na Havard a matsayin ministan lafiya, mukamin da Dr Osagie Ehanire daga karamar hukumar Oredo na jihar Edo ya rike.

Kara karanta wannan

Ministan Buhari, Lai Mohammed Ya Sake Samun Shirgegen Matsayi Mai Muhimmanci, Ya Yi Godiya

Wanene Pate?

Muhammad Ali Pate ya kasance shahararren likitan Najeriya, kwararren a fannin kiwon lafiya, kuma jigo a bangaren lafiya ta duniya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya bayar da gudunmawa sosai a ma'aikatar lafiya a nan gida Najeriya da ma duniya.

Da ilimin likitanci, Pate ya sadaukar da aikinsa wajen inganta tsarin lafiya da magance kalubalen da harkar lafiya ke fuskanta ta bangaren ci gaba.

Pate ya yi aiki a matsayin karamin ministan lafiya a Najeriya daga 2011 zuwa 2013, inda ya taka muhimmiyar rawar gani wajen aiwatar da sauye-sauye da tsare-tsare a fannin kiwon lafiya.

Tsohon ministan Jonathan ya ki amsar mukami na duniya saboda tayin da Tinubu ya yi masa

A gefe guda, Legit.ng ta kawo a baya cewa tsohon karamin ministan lafiya, Muhammad Pate, na iya zama daya daga cikin ministocin shugaban kasa Bola Tinubu bayan an yi wasu sabbin sanarwa a ranar Litinin, 26 ga watan Yuni.

Har yanzu shugaban kasa Tinubu wanda ya kama aiki a matsayin shugaban kasar Najeriya na 16 a ranar 29 ga watan Mayu bai mika jerin sunayen ministocinsa ga majalisar dokokin kasa ba kamar yadda doka ta bayyana, jaridar Premium Times ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng