El-Rufai Na Iya Zama Ministan Wutar Lantarki Yayin da Jerin Sunayen Ministoci Ya Gaban Majalisa
- Wata majiya ta yi karin haske kan aikin da za a iya ba tsohon ministan birnin tarayya, Mallam Nasir El-Rufai
- An tattaro cewa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya mika jerin sunayen ministocinsa gaban shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio a safiyar nan
- A cewar majiyar, El-Rufai na iya zana sabon ministan wutar lantarki a gwamnatin Shugaban kasa Tinubu
Rahotanni sun kawo cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai, ya samu shiga jerin ministocin Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
Kamar yadda jaridar The Nation ta rahoto, wata majiya a majalisar dattawa ta ce shugaban kasa Tinubu ya gabatar da jerin sunayen gaban Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio a safiyar nan don cika wa'adin kwanaki 60 da kundin tsarin mulki ya ba shi.
Majiyar ta bayyana cewa ana iya mikawa El-Rufai ragamar kula da ma'aikatar wutar lantarki.
Ku tuna cewa, El-Rufai ya rike kujerar tsohon ministan babban birnin tarayya Abuja a mulkin tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
An Gama Komai, El-Rufai, Wike, Oyetola da Edun Za Su Zama Ministocin Bola Tinubu
Legit.ng ta kawo a baya cewa Idan abubuwa ba su canza a halin yanzu ba, an jima kadan Bola Ahmed Tinubu zai aikawa majalisar dattawa sunayen Ministocinsa.
Vanguard a rahoton da ta fitar dazu, ta ce shugaban Najeriyan ya zabi mutane 43 da yake so Sanatoci su tantance a matsayin Ministocin tarayya.
Daga cikin wadanda aka samu kishin-kishin cewa za a bada sunansu a yau akwai tsohon Gwamnan jihar Kaduna watau Malam Nasir El-Rufai.
Majiyoyi sun bayyana Wanda zai zama ministan shari'a Kuma atoni janar a gwamnatin Tinubu
A wani labarin, mun ji cewa Shugaban kasa Bola Tinubu ya shirya gabatar da jerin sunayen ministocinsa a gaban majalisar dokokin tarayya a yau Alhamis, 27 ga watan Yuli.
Wasu majiyoyi sun bayyana cewa akwai yiwuwar Lateef Fagbemi zai zama zabin shugaban kasa Tinubu domin ya zama Atoni Janar na tarayya kuma ministan shari'a, rahoton Vanguard.
Fagbemi ya kasance lauyan da ke kare jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a shari'ar zaben shugaban kasa da ke gudana a kotu.
Asali: Legit.ng