"Tsohon Shugaban Majalisa Ya Jawowa Abdullahi Adamu Rasa Shugabacin APC"
- Salihu Lukman ya yi bayani a kan abin da ya kira fitinar da ke bin APC daga wannan zuwa wannan
- Mataimakin shugaban jam’iyyar ta APC ya ce an yi kokarin ba Ahmad Lawan tikiti a zaben 2023
- A ra’ayin Lukman, Abdullahi Adamu da sakatarensa sun yi kama-karya da su ke rike da majalisar NWC
Abuja - Mataimakin shugaban APC na Arewa maso yamma, Salihu Lukman ya ce kama-karyar da aka tafka ya yi sanadiyyar tafiyar Abdullahi Adamu.
Alhaji Salihu Lukman ya ce abubuwa sun munana a jam’iyyar APC mai-ci a karkashin jagorancin Sanata Abdullahi Adamu, har ta kai ya yi murabus.
Vanguard ta ce jigon jam’iyyar ya zargi tsohon shugaban na su da yunkurin kakaba wanda zai tsaya masu takarar shugaban kasa a zaben da ya gabata.
Ganduje vs Al-Makura: Malamin Addini Ya Bayyana Wanda Ya Kamata APC Ta Nada a Matsayin Shugabanta Na Kasa
Neman ba Ahmad Lawan tuta
Baya ga hana kowa motsawa a APC, Lukman ya ce Sanata Adamu ya yi nufin ganin Ahmad Lawan ya samu tikiti, amma Gwamnoni su ka tsaida shi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A lokacin Lawan ya na shugaban majalisar dattawa, shi ma Asiwaju Bola Tinubu ya na neman tikiti, shugaban na APC ya karkata ga tsohon abokin aikinsa.
Wani jawabi da tsohon shugaban na PGF ya fitar, ya nuna jam’iyyar da ke mulkin kasar ta na cigaba da tsumbulawa daga wannan rikici zuwa wannan.
An rahoto Lukman yana cewa majalisar NWC ta nesanta kan ta daga maganar zaben sabon shugaban da zai jagoranci jam’iyya a madadin Sanata Adamu.
Yadda aka samu matsala a APC
"Jim kadan bayan an yi nasarar shirya babban zaben da ya kawo majalisar NWC a karkashin jagorancin Abdullahi Adamu, sai APC ta koma gidan jiya.
An toshe sauran bangarorin jam’iyya. Babu taron da ake gudanarwa, kuma majalisar NWC ta zama ‘yar kallo, shugaban jam’iyya da sakatare su ke komai.
Abin ya kai intaha da shugaban jam’iyya na kasa ya yi kokarin kakaba Sanata Ahmad Lawan a matsayin ‘dan takaran shugaban kasa na jam’iyya a 2023."
- Salihu Lukman
Har zuwa yanzu Lukman yana nan a kan bakarsa na cewa daga Arewa ta tsakiya za a fito da sabon shugaba, maimakon a nada Dr. Abdullahi Umar Ganduje.
Lukman bai goyon bayan Abdullahi Ganduje
Bayan ya fito ya yi magana a gaban Duniya, sai aka ji labari Salihu Luman ya rubutawa Kungiyar PGF wasika a kan batun Dr. Abdullahi Ganduje.
An ji shugaban jam’iyyar yana kira ga Gwamnoni su sake tunani game da shugabanci, ya ce babu adalci idan aka yi watsi da Arewa ta tsakiya.
Asali: Legit.ng