Majalisar Dokokin Kaduna Ta Dakatar Da Shugabannin Kananan Hukumomi 3 Bisa Zargin Almundahana

Majalisar Dokokin Kaduna Ta Dakatar Da Shugabannin Kananan Hukumomi 3 Bisa Zargin Almundahana

  • Majalisar Dokokin jihar Kaduna ta dakatar da shugabannin ƙananan hukumomi uku bisa zargin aikata almundahana
  • Majalisar ta zargi shugabannin da saɓawa dokokin jihar Kaduna wajen tafiyar da al'amuran ofisoshinsu
  • An umarci shugabannin ƙananan hukumomin da abun ya shafa da su miƙa ragamar shugabancin nasu ga mataimakansu

Kaduna - Majalisar Dokokin jihar Kaduna ta sanar da dakatar da wasu shugabannin ƙananan hukumomin jihar su uku bisa zarginsu da almundahana.

An bayyana sanarwar dakatarwar tasu a zaman majalisar na ranar Talata, 25 ga watan Yuli kamar yadda Daily Trust ta wallafa.

Majalisar Kaduna ta sanar da dakatar da shugabannin kananan hukumomin uku na jihar
Majalisar Dokokin jihar Kaduna ta dakatar da shugabannin kanan hukumomi uku daga kujerunsu. Hoto: Kaduna State Assembly
Asali: Facebook

Dalilin da ya sa aka dakatar da shugabannin ƙananan hukumomin

An zargi shugabannin ne da bayar da kwangiloli ba tare da bin ƙa’idojin da suka dace ba, kamar yadda dokokin jihar ta Kaduna suka tanada.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Hankula Sun Tashi Bayan Wata Katanga Ta Rufto Kan Wasu Yara, An Samu Asarar Rai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamitin wucin gadi kan binciken wanda mamba mai wakiltar yankin Lere ta Gabas, Munirat Sulaiman Tanimu ta jagoranta, ya yi nazari sosai kan harkokin kuɗi na ƙananan hukumomin Chikun, Kaura, Kagarko, Soba, da Birnin Gwari.

Majalisar ce ta ba da umarnin gudanar da binciken, bayan wani ƙuduri da aka cimmawa a ranar 18 ga Yulin shekarar 2023.

Yadda aka gudanar da bincike a kan shugabannin

Munirat ta ce sun nemi shugabannin ƙananan hukumomin da abin ya shafa, da su gabatar da bayanan duka kuɗaɗen da aka kashe a aika-aikace a ƙananan hukumomin nasu tun daga wata Yunin 2022 zuwa Yin 2023.

Ta ƙara da cewa bayan nazarin takardun ne suka gano cewa shugabannin Kaura, Kagarko, da Chikun sun sabawa sashe na 48 na dokar gudanar da ƙananan hukumomi na shekarar 2018, da sashe na 35 da ƙaramin sashe na 25 na dokar kadarorin gwamnatin jihar Kaduna na shekarar 2016.

Kara karanta wannan

Jerin Sunaye: Gwamnan Arewa Ya Fusata, Ya Tsige Sarakuna 6 Daga Karagar Mulki Kan Wasu Laifuka

Ta kuma ce waɗannan sassa sun zayyana yadda ya dace a kasafta kuɗi da kuma ka’idojin siyar da kayayyakin gwamnatin jihar kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Sakamakon haka ne kwamitin ya ba da shawarar cewa, shugabannin uku su bar ofisoshinsu na tsawon watanni shida masu zuwa don ci gaba da bincike, sannan su miƙa ragamar shugabancin ga mataimakansu.

Uba Sani ya yi sabbin naɗe-naɗe a gwamnatinsa

Legit.ng ta yi rahoto a baya, kan wasu muhimman sababbin naɗe-naɗe da gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani ya yi.

Gwamna Uba Sani dai ya sanar da naɗin sabbin shugabannin hukumomi, manyan masu ba da shawara na musamman da kuma hadiman da za su riƙa taimaka masa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng