"Mamban APC" Ta Fadi Sunayen Mutum 3 Da Aka Cire Daga Cikin Ministocin Tinubu

"Mamban APC" Ta Fadi Sunayen Mutum 3 Da Aka Cire Daga Cikin Ministocin Tinubu

  • Ruɗanin da ke tattare da sunayen Ministocin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu da ake dako ya ƙara buɗe sabon shafi
  • Wani kishin-ƙishin ya nuna cewa an cire sunayen wasu jiga-jigan siyasa 3 bayan da fari sunansu ya shiga cikin ministocin
  • Sunayen da ake zargin an cire sun haɗa da Nyesom Wike, Abdullahi Umar Ganduje da Atiku Bagudu, tsoffin gwamnonin Ribas, Kano da Kebbi

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Sabon ƙishin-kishin ya bayyana dangane da sunayen ministocin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, wanda har yanzu ake dakon fitowarsa.

A sabon bayani kan sunayen ministocin, an gano cewa an cire sunayen wasu jiga-jigan siyasa uku daga cikin Ministocin da shugaba Tinubu ke shirin miƙa wa majalisa.

Wike, Ganduje da Atiku Bagudu.
"Mamban APC" Ta Fadi Sunayen Mutum 3 Da Aka Cire Daga Cikin Ministocin Tinubu Hoto: Nyesom Ezenwo Wike, Sen Abubakar Bagudu da Abdullahi Ganduje
Asali: Facebook

Jerin sunayen mutum 3 da aka cire

Sunayen jiga-jigan da aka cire sun haɗa da tsohon gwamnan jihar Ribas kuma jigon babbar jam'iyyar adawa PDP, Nyesom Wike, da tsohon gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Cire Wike da Ganduje Daga Cikin Jerin Ministoci? Gaskiya Ta Yi Halinta

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ɗayan jigon da aka zare sunansa daga cikin ministocin shugaba Tinubu shi ne tsohon gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu.

Wannan na ƙunshe ne a wani ɗan gajeren saƙo da Sa'adatu Macciɗo, mambar jam'iyar All Progressive Congress watau APC ta wallafa a shafinta na Tuwita.

A saƙon wanda Legit.ng Hausa ta gani ranar Talata, 25 ga watan Yuli, 2023, Macciɗo ta rubuta cewa:

"Bagudu, Wike da Ganduje sun fita daga cikin jerin sunayen Ministocin shugaban ƙasa."

Wannan na zuwa ne awanni bayan jigon APC kuma shugaban ƙungiyar magoya bayan Tinubu ya musanta raɗe-raɗin cire sunan Ganduje da Wike.

A wata hira, Kodinetan ƙungiyar Tinubu Vanguard (BAT-V) ya roƙi ɗaukacin al'umma da su yi fatali da labarin domin ba shi da tushe balle makama.

Kotu Ta Bada Belin Dakataccen Gwamnan CBN, Godwin Emefiele

Kara karanta wannan

Rikicin APC: Tsohon Gwamna Zai Maye Gurbin Omisore a Kujerar Sakataren Jam'iyyar Na Kasa? Bayanai Sun Fito

A wani rahoton Babbar kotun tarayya mai zama a Ikoyi, jihar Legas ta bada belin dakataccen gwamnan CBN, Godwin Emefiele kan kuɗi N20m.

Sharuɗɗan da Kotun ta gindaya na belin sun haɗa da gabatar da wanda zai tsaya masa, wanda ya mallaki kadarori a kewayen inda Kotu ke zama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262