Bala Muhammad Ya Aike da Sunayen Kwamishinoni 24 Ga Majalisar Dokokin Bauchi
- Gwamnan Bauchi, Bala Muhammad, ya nada kwamishinoni 24 kuma ya aika sunayensu zuwa majalisar dokokin jihar
- Kakakin majalisa, Abubakar Y. Suleiman, ya karanto jerin sunayen kwamishinonin da gwamnan ya aiko a zaman ranar Litinin
- Majalisar za ta tantance wadanda aka mika mata sunayensu a tsakanin 2, 3 da 4 ga watan Agusta mai kamawa
Bauchi - Gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad, ya aike wa majasar dokokin jihar da sunayen mutanen da yake son nada wa kwamishinoni.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa gwamnan ya tura sunayen mutane 24 ga majalisar dokokin Bauchi domin tantance su da kuma tabbatar da su a matsayin kwamishinoni.
Kakakin majalisar, Abubakar Y. Suleiman, ne ya karanta sakon mai girma gwamna a zaman majalisar na ranar Litinin, 24 ga watan Yuli.
Da yake karanto wasikar, ya ce sun samu sako daga gwamna inda ya nemi su tantance da tabbatar da nadin mutanen a matsayin kwamishinoni kuma mambobin majalisar zartarwa na jihar daidai da tanadin kundin tsarin mulki na 199.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jerin sunayen kwamishinonin
Shugaban masu rinjaye a majalisar, Saleh Hodi Jibir, ya karanto sunayen wadanda aka nada kamar haka:
- Maiwada Bello
- Ibrahim Gambo (Alkaleri)
- Mahmoud Babamaji Abubakar
- Danlami Ahmed Kawule (Bauchi)
- Tsammani Lydia Haruna (Bogoro)
- Ahmed Sarki Jalam (Dambam)
- Yakubu Ibrahim Hamza (Darazo)
- Usman Santuraki (Dass)
- Abdul Hassan Gamawa
- Muhammad Salees (Gamawa)
- Dr Yakubu Adamu (Giade)
- Usman Abdulkadir Moddibo (Jama’are)
- Hajara Jibrin Gidado (Itas/Gadau)
- Farouk Mustapha (Katagum)
- Hajara Yakubu Wanka (Kirfi)
- Aminu Hammayo (Misau)
- Hassan El-Yakub (Ningi)
- Muhammad Hamisu Shira (Shira)
- Simon Madugu Yalams
- Abubakar Abdulhamid Bununu (Tafawa Balewa)
- amila Muhammad Dahiru
- Adamu Umar Sambo (Toro)
- Abdulrazak Nuhu Zaki
- Amina Muhammad Katagum (Warji)
Yaushe za a tantance kwamishinonin da aka nada?
Majalisar ta yanke shawarar tantance wadanda aka nada a ranakun 2,3 da 4 ga watan Agustan 2023, rahoton Nigerian Tribune.
Jam'iyyar PDP na zargin APC da hannu a harin da aka kaiwa Atiku a Adamawa
A wani labari na daban, mun ji cewa jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta zargi jam'iyyar All Progressives Congress (APC) da alhakin kitsa harin da aka kaiwa dan takararta na shugaban kasa a zaben 2023, Atiku Abubakar.
A ranar Lahadi, 23 ga watan Yuli, wasu da ake zaton yan Boko Haram ne suka farmaki tsohon mataimakin shugaban kasar a gidansa da ke garin Yola, babban birnin jihar Adamawa kuma mahaifarsa.
Asali: Legit.ng