PDP Ta Hadu Da Gagarumin Cikas Yayin da Jiga-Jiganta 63 Suka Sauya Sheka Zuwa APC a Ondo
- Babbar jam'iyyar adawa ta PDP ta rasa wasu manyan jiga-jiganta inda suka koma jam'iyyar ll Progressives Congress (APC) mai mulki
- Mambobin jam'iyyar PDP 63 sun sauya sheka daga jam'iyyar zuwa APC a karamar hukumar Idanre ta jihar Ondo
- Masu sauya shekar sun bayyana cewa komawarsu APC zai kara karfafa damar da jam'iyyar ke da shi a zaben gwamna da na kananan hukumomi da za a yi a 2024
Jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) ta hadu da gagarumin tangarda a sansaninta.
Hakan ya kasance ne yayin da jiga-jigan PDP 63 suka sauya sheka zuwa jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki a karamar hukumar Idanre ta jihar Ondo a ranar Juma'a, 21 ga watan Yuli.
Cikakken bayanan jiga-jigan PDP da suka sauya sheka zuwa APC ya bayyana
Wadanda suka sauya shekar sun hada da shugaban kungiyar dattawan PDP a yankin, Idowu Akinseye, tsohon mai ba da shawara ta musamman ga tsohon gwamna Olusegun Mimiko, Marcus Adeoti, Lad Owoseni, tsohon shugaban kungiyar 'Timber Finishers', Brigadier Omogbemi, jaridar The Nation ta rahoto.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Cif Banji Kuroloja, tsohon sakataren marigayi Cif Obafemi Awolowo, Cif Korede Duyile da Farfesa John Jejela, da dai sauransu.
Sai dai sun bayyana cewa sauya sheka zuwa jam’iyya mai mulki zai kara wa APC karfi a zaben kananan hukumomi da na gwamna da za a yi a shekara mai zuwa.
Shugaban APC ya tarbi wadanda suka sauya sheka daga PDP
Da yake magana a kan ci gaban, , shugaban jam’iyyar APC na Ondo, Injiniya Ade Adetimehin, wanda ya tarbi wadanda suka sauya shekar, ya ce su yan siyasa ne da ke tabbatar da nasarar jam’iyyar PDP a duk lokacin zabe, rahoton Daily Independent.
Ya bayyana cewa da wannan sauya shekar da suka yi zuwa jam'iyyar, Idanre da kewaye sun zama na APC.
Uba Sani ya ce duk yaudara ce shirin rabawa yan Najeriya N8,000
A wani labari na daban, Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya bayyana shirin rabawa yan Najeriya tallafin kudi N8,000 da gwamnatin Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ke yunkurin yi a matsayin yaudara.
Tinubu ya yanke shawarar turawa iyalai miliyan 12 N8,000 na tsawon watanni shida domin rage masu radadin cire tallafin man fetur.
Asali: Legit.ng