Bayan Tsawon Lokaci, Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa Ta Zaɓi Sabon Kakaki

Bayan Tsawon Lokaci, Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa Ta Zaɓi Sabon Kakaki

  • Bayan tsawon lokaci ana taƙaddama kan shugabanci, majalisar dokokin Nasarawa ta zaɓi sabon shugaba da mataimaki
  • A zaman yan majalisar na ranar Jumu'a a Lafiya, sun zaɓi Honorabul Balarabe a matsayin shugaban majalisa ta 7
  • Wannan ya biyo bayan tarukan neman sulhu da aka gudanar tsakanin tsagin Ogazi da Balarabe wanda ya haifar da ɗa mai ido

Nassarawa - Rigingimun shugabanci a majalisar dokokin jihar Nasarawa sun zo karshe yayin da Honorabul Daniel Ogazi ya sauka daga matsayin kakakin majalisar.

Channels tv ta rahoto cewa bayan saukarsa, mambobi suka sake zaɓen Ibrahim Balarabe a matsayin wanda zai cike gurbin shugaban majalisar dokokin jiha ta 7 a tarihi.

Rikicin majalisar dokoki ya zo karshe a jihar Nasarawa.
Bayan Tsawon Lokaci, Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa Ta Zaɓi Sabon Kakaki Hoto: channels
Asali: Facebook

Baki ɗaya mambobi 24 na majalisar sun halarci zaman ranar Jumu'a a Lafiya, babban birnin jihar Nasarawa bayan jerin zaman sulhu tsakanin tsagin Ogazi da tsagin Balarabe.

Kara karanta wannan

Daga Karshe, Majalisar Dattawa Ta Yi Magana Kan Sunayen Ministocin Shugaba Bola Tinubu

Bayan cimma matsaya da samun sulhu a tsakaninsu, a zaman 'yan majalisa na jiya Jumu'a aka zaɓi Balarabe, mamba mai wakiltar Umaisha/Ugya a matsayin shugaba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har ila yau mambobin majalisar sun zabi Honorabul Abel Yakubu Bala mai wakiltar mazaɓar Nasarawa Eggon ta yamma a matsayin mataimakin kakakin majalisa.

Muƙaddashin magatakardan majalisar, Ibrahim Musa, shi ne ya sanar da haka yayin rantsar da mambobin a zauren majalisar da ke Lafiya, babban birnin jiha.

Magatakardar ya ce wannan ci gaban ya yi daidai da sanarwar Gwamna Abdullahi Sule da kuma kundin tsarin mulkin Tarayyar Najeriya.

Daga nan kuma sai ya rantsar da sabbin shugabannin biyu, daga bisani kuma Honorabul Balarabe ya rantsar da sauran mambobin majalisa.

Zamu tafi da kowa a harkar shugabanci - Balarabe

A jawabinsa na karɓan mulki, Balarabe ya yi alkawarin samar da shugabancin haɗin kai domin tabbatar da da zaman lafiya da ci gaban jihar Nasarawa.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Ɗan Majalisar Tarayya Ya Yi Mummunan Hatsari a Hanyar Koma Wa Abuja

Punch ta rahoton kakakin majalisar na cewa:

“Ina taya ’yan uwa masu girma murnar rantsar da ku da kuma gode muku bisa zabe na a matsayin kakakin majalisa ta bakwai."
“Na jagoranci al’amuran wannan majalisa tsawon shekaru takwas da suka gabata cikin adalci da tsoron Allah. Ina so in tabbatar muku cewa zan ci gaba a kan wannan tafarkin."
"Zan kuma ci gaba da tsarin da kuka sani kofa a buɗe ga kowa kamar yadda na yi a cikin shekaru takwas da suka gabata,"

Majalisar Dattawa Ta Yi Magana Kan Sunayen Ministocin Shugaba Bola Tinubu

A wani labarin kuma jinkirin shugaba Bola Tinubu wajen miƙa sunayen Ministoci ka iya tilasta wa majalisar dattawa ɗaga hutunta na shekara-shekara.

Sanatoci na tsammanin shugaba Bola Ahmed Tinubu zai aiko da sunayen ministocin a farkon mako mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262