Cire Tallafi: CAN Ta Shawarci Tinubu Kan Ba Da Tallafi, Ta Ce Ba Iya Kudi Ya Kamata a Rabawa Mutane Ba
- Kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN), ta shawarci Shugaba Tinubu dangane da rabon kayan tallafin da yake son yi wa 'yan Najeriya
- Ta ce ba iya rabon kudade ya kamata Shugaba Tinubu ya fi mayar da hankalinsa a kai ba
- CAN ta shawarci shugaban da ya samar da ababen hawa domin saukaka harkokin sufuri a duka jihohin Najeriya
Abuja - Kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN), ta shawarci Tinubu da kar ya tsaya iya kan rabon kudi a wajen bayar da tallafin da yake shirin yi.
Shugaban kungiyar ta CAN na kasa, Daniel Okoh ne ya bayyana haka ranar Juma'a a Abuja kamar yadda The Punch ta ruwaito.
CAN ta shawarci Tinubu ya sanya tallafin a harkokin sufuri
CAN ta shawarci gwamnatin ta Tinubu da ta duba yiwuwar samar da ababen hawa domin saukaka harkokin sufuri a duk jihohin Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ta ce hakan zai yi tasiri matuka wajen rage yawan kudaden da mutane ke kashewa a zirga-zirga ta yau da kullum.
Haka nan CAN ta shawarci gwamnatin ta Tinubu da ta yi kokarin daukar matakan da za su taimaka wajen saukar farashin man fetur a Najeriya.
Daga cikin irin matakan a cewar kungiyar ta CAN, akwai cire duk wasu haraje-haraje da ake kakabawa masu shigo da man daga waje.
CAN ta yabawa Tinubu kan yadda yake raba mukaman gwamnati
Daniel Okoh ya ce yanayin kamun ludayin mulkin Shugaba Tinubu daga farkon hawansa zuwa yanzu abin a yaba ne.
Daniel ya kara da cewa nade-naden sabbin hafsoshin tsaron da Shugaba Tinubu ya yi a kwanakin baya ya tabbatar da cewa za a yi wa kowane bangaren kasar nan adalci.
A dalilin hakan ne kungiyar ta CAN ta jinjinawa shugaban kasa Bola Tinubu, inda ta ce ya dauko hanyar hada kan 'yan Najeriya da kuma samar da zaman lafiya da ci gaban kasa baki daya.
CAN ta kuma kara da cewa duk da a bayyane yake cewa cire tallafin man fetur ya zama dole, ta ce yana da kyau a ce gwamnati ta aiwatar da shirin ta yadda ba zai jefa 'yan kasa cikin yanayi ba.
Business Day a kwanakin baya ta yi wani rahoto da ke nuna yadda gwamnatin Tinubu ke shan suka dangane da rabon tallafin naira 8,000 da ta ce za ta yi ga 'yan Najeriya miliyan 12 na tsawon watanni shida.
Gani Adams ya caccaki Tinubu kan cire tallafin man fetur
Legit.ng a baya ta kawo muku rahoto kan basarake kuma mai fada a ji a yankin Yarabawa, Cif Gani Adams da ya soki Tinubu dangane da cire tallafin man fetur.
Adams ya ce 'yan Najeriya da suka tsabi Tinubu matsayin shugaban kasa ba su yi tsammanin shan irin wannan wahalar ba.
Asali: Legit.ng