Shugabancin APC: Maye Gurbin Adamu Da Ganduje Zai Kashe Jam'iyyar, Jigon APC Ya Yi Bayani

Shugabancin APC: Maye Gurbin Adamu Da Ganduje Zai Kashe Jam'iyyar, Jigon APC Ya Yi Bayani

  • Babban jigo a jam'iyyar APC, Salihu Lukman, ya ce bai wa Ganduje shugabancin APC zai janyo matsala a jam'iyyar
  • Lukman wanda mataimakin shugaban APC na kasa na shiyyar Arewa maso Yamma ne ya ce ba adalci ba ne dauke kujerar daga yankin Arewa ta Tsakiya
  • Ya kara da cewa bai wa Ganduje mukamin zai wargaza tsarin raba mukamai na shiyya-shiyya na jam'iyyar ta APC

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Mataimakin jam'iyyar APC na kasa shiyyar Arewa maso Yamma, Saihu Lukman, ya ce baya goyon bayan a bai wa Ganduje shugabancin jam'iyyar.

Ya bayyana cewa bai wa Ganduje shugabancin APC daidai yake da ruguza jam'iyyar.

Akwai kishin-kishin din cewa Shugaba Tinubu ya bayyana ra'ayinsa na bai wa Ganduje shugaban jam'iyyar APC na kasa kamar yadda Daily Trust ta wallafa.

Kara karanta wannan

"APC Za Ta Mutu Murus": Abin da Yan Najeriya Ke Cewa Kan Rade-Radin Maye Gurbin Adamu Da Ganduje a Matsayin Shugaban APC

Salihu Lukman ya ce bai kamata a bai wa Ganduje shugabancin APC ba
Salihu Lukman ya ce bai wa Ganduje shugabancin APC ya saba da tsarin jam'iyya, zai kuma kasheta gaba daya. Hoto: Maje El-Hajeej Hotoro
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

APC ba ta koyi darasi ba daga abubuwan da suka faru a baya

Sai dai a nasa ra'ayin, Lukman na ganin tsaida Ganduje domin kujerar tun kafin aiwatar da babban taron jam'iyyar bai dace ba kwata-kwata.

Lukman wanda yana daga cikin wadanda ba sa goyon bayan Abdullahi Adamu, ya kara da cewa indai har maganar da ake yi ta tabbata, to sauyin shugabancin da akai ba shi da wani amfani, kuma jam'iyyar ba ta koyi darasi ba.

Lukman ya ce bai wa Ganduje shugabancin ya nuna ba a dauki mambobin jam'iyyar da muhimmanci ba.

Ya kuma bayyana cewa hakan zai hargitsa duk tsarin raba mukamai na shiyya-shiyya da jam'iyyar ta yi, wanda da shi ne aka kafa shugabancin majalisun tarayya.

Ba adalci ba ne dauke kujerar shugabancin jam'iyyar daga Arewa ta Tsakiya

Kara karanta wannan

Ba a Tausayin Talaka: PDP Ta Yiwa Tinubu da APC Wankin Babban Bargo Kan Tsadar Mai

Lukuman ya kara da cewa rashin adalci ne a dauke kujerar shugabancin jam'iyyar daga Arewa ta Tsakiya a mayar da shi Arewa maso Yamma.

Ya kafa hujja da cewa kakakin Majalisar Wakilai da kuma mataimakin shugaban Majalisar Dattawa duk sun fito ne daga shiyyar Arewa maso Yamma, kamar yadda Vanguard ta wallafa.

A saboda haka ne Lukman ya ce ya kamata a yi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da shugabancin jam'iyyar a Arewa ta Tsakiya ba wani yanki daban ba.

Jam'iyyar PDP ta caccaki APC kan tsadar man fetur

Legit.ng a baya ta yi rahoto cewa jam'iyyar adawa ta PDP ta caccaki jam'iyyar APC mai mulki kan hauhawar farashin man fetur a Najeriya.

Jam'iyyar ta PDP ta ce bai kamata a ce 'yan Najeriya na shan man fetur kan abinda ya wuce naira 150 ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng