Kashim Shettima Ya Roki Tsofaffin Sanatoci Su Marawa Shugaba Tinubu Baya

Kashim Shettima Ya Roki Tsofaffin Sanatoci Su Marawa Shugaba Tinubu Baya

  • Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima, ya nemi tsofaffin sanatoci da su marawa Tinubu baya
  • Shettima ya bayyana hakan ne a yayin da yake zantawa da sanatoci na Majalisar Dattawa ta Tara a Abuja
  • Sanatocin sun yi wa gwamnatin Tinubu fatan samun nasara, gami da ba da tabbacin samun cikakken goyon bayansu

Abuja - Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya buƙaci tsofaffin sanatoci da su bai wa gwamnatin Shugaba Tinubu goyon baya.

Ya miƙa wannan buƙata ne ranar Laraba, 19 ga watan Yuli, yayin da yake zantawa da tsofaffin sanatocin na majalisa ta tara a fadar Gwamnatin Tarayya da ke Abuja kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Shettima ya gana da tsofaffin sanatoci
Shettima ya nemi tsofaffin sanatoci su marawa Tinubu baya. Hoto: Kashim Shettima
Asali: Facebook

Shettima ya ce zai ci gaba da kasancewa da tsoffin abokan aikinsa

A wata sanarwa da daraktan yaɗa labaran ofishin mataimakin shugaban ƙasar Olusola Abiola ya fitar, ya bayyana cewa Tinubu mutumin kirki ne, don haka ne ma yake neman sanatocin su ba shi goyon baya.

Kara karanta wannan

Sauki Ya Zo: Shugaba Tinubu Ya Gana Da Manyan Kusoshi a Kasar Nan Domin Tsamo Talaka Daga Halin Kunci, Bayanai Sun Fito

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shettima ya bayyana cewa a zaman da ya yi a Majalisar Dattawa ta tara, ya haɗu da mutanen da ya ƙulla abota tare da su, waɗanda kuma zai ci gaba da hulɗoɗin arziƙi tare da su har ƙarshen rayuwarsa.

Ya kuma ba su tabbacin cewa zai yi aiki tare da su domin ciyar da ƙasar gaba, saboda a cewarsa abinda ya haɗa su ya fi abinda ya raba su.

Sanatocin sun yi wa gwamnatin Tinubu fatan samun nasara

Shugaban tawagar tsoffin sanatocin, Sanata Philip Aduda ya tabbatar da ba da cikakken goyon bayansu ga gwamnatin ta Tinubu.

Ya kuma yi wa gwamnatin addu'ar samun nasara wajen aiwatar da sabbin tsare-tsare da ƙudurorin da ta zo da su kamar yadda jaridar Leadership ta wallafa.

Wani daga cikin tawagar, Sanata George Sekibo, ya nuna ƙwarin gwiwarsa cewa Shettima yana da cikakkiyar gogewar da zai tabbatar da nasarar tsare-tsaren da Shugaba Tinubu ya zo da su.

Kara karanta wannan

"Matata Tana Zabga Mun Mari Ta Lakaɗa Mun Duka Kamar Jaki" Ɗan Kasuwa Ya Nemi Saki a Kotu

Daga cikin tawagar akwai Sanata Sam Egwu, Sanata Aliyu Abdullahi, Sanata Gabriel Suswam, Sanata Emmanuel Bwacha, Sanata Chukwuma Utazi, Sanata Yakubu Oseni, Sanata Jarigbe Agom Jarigbe, Sanata Suleiman Kwari, da Sanata Stella Oduah.

An bayyana yiwuwar Ganduje zai zama sabon shugaban jam'iyyar APC

Legit.ng ta kawo muku rahoto a baya cewa, alamu sun nuna cewa akwai yiwuwar tsohon gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya maye gurbin Abdullahi Adamu a matsayin sabon shugaban jam'iyyar APC na ƙasa.

Rahotanni sun nuna cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da makusantansa, sun nuna goyon bayan Ganduje ya zama sabon shugaban jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng