Yanzu: Dirama Yayin Da EFCC Ta Ce Bata San Lauyanta Ba A Kotu, Ta Bada Dalili

Yanzu: Dirama Yayin Da EFCC Ta Ce Bata San Lauyanta Ba A Kotu, Ta Bada Dalili

  • Hukumar yaki da rashawa cikin sabon karar da ta shigar kan tsohuwar minista Stella Oduah, ta ce Ibrahim Mohammed, mai kiran kansa lauyanta, ita ya ke yi wa aiki ba
  • H.A. Okonofua, lauyan EFCC, ne ya fada wa babban kotun tarayya da ke Abuja a cikin sabuwar karar da Mohammed ya shigar kan Oduah
  • Sabon karar na da alaka da yin karya da gabatar da takardun bogi

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Hukumar Yaki da Rashawa (EFCC) ta ce bata san lauyanta, Ibrahim Mohammed ba, wanda ya shigar da kara kan Stella Oduah, tsohuwar ministan sufurin jiragen sama, da sunan hukumar yaki da rashawar.

Sabon karar da aka shigar na da alaka ne da karya da kuma takardun bogi, The Tribune ta rahoto.

Kara karanta wannan

Tsagerun 'Yan Bindiga Sun Buɗe Wa Mutane Wuta a Gargruwa 2, Sun Halaka Mutane da Yawa

EFCC ta ce ba ta aiki lauyanta kotu ba ya shigar da kara ba kan Oduah
EFCC Ta Ce Bata San Lauyanta Ba A Kotu Game Da Kara Kan Oduah. Hoto: EFCC
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Abin da yasa EFCC ta ce bata san lauyanta ba

Amma a ranar Talata, 18 ga watan Yuli, H.A. Okonofua, lauyan EFCC, ya sanar da babban kotun tarayya da ke Abuja cewa hukumar yaki da rashawar ba ta san komai game da karar da Mohammed ya shigar kan Oduah ba.

Tsohuwar ministan ba ta halarci zaman kotun ba, amma Okonofua, a farkon shari'ar, ya fada wa Mai Shari'a James Omotosho, alkalin kotun, cewa binciken da hukumar ta yi ya nuna cewa, "an mayar da Ibrahim Mohammed zuwa Rundunar Yan sanda a ranar 14 ga watan Nuwamban 2022, kuma ba a tura shi ya wakilci EFCC ba don karar wacce aka shigar da kara."

Amma Mai Shari'a Omotosho ya fada wa Okonofua cewa ba a kawo wa kotu wannan rahoton ba kuma lauyan ya amsa cewa an yi lattin cike rahoton.

Kara karanta wannan

Hadiman Majalisa za su Lakume N16bn, Tinubu da Shettima za su ci Abincin N500bn

Kotu ta dage fara sauraron sabon kara tsakanin EFCC da Stella Oduah

An dage fara sauraron karar zuwa ranar 4 ga watan Oktoba, lokacin an gabatarwa kotun rahoton binciken.

Kuma, tsohuwar ministan a bangarenta ta ce ba ta san an shigar da sabon kara a kanta ba.

Oduah, a baya ta wakilci Anambra ta Arewa a Majalisar Tarayya kuma ta ce Rundunar Yan sada ko wata Hukumar Tsaro ba ta taba bincikar ta ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164