Jigon PDP Bode George Ya Ce Najeriya Ta Shiga Halin Da Take Ciki Ne Saboda Kwaikwayon Amurka

Jigon PDP Bode George Ya Ce Najeriya Ta Shiga Halin Da Take Ciki Ne Saboda Kwaikwayon Amurka

  • An bayyana cewa tsarin mulkin da ake tafiyar da Najeriya a halin yanzu ne ya janyo wahalhalun da ake ciki
  • Tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa, Cif Bode George ne ya bayyana haka wajen taro a Legas
  • Jigon na PDP ya ce an kwafo tsarin da ake kai a yanzu ne daga kundin tsarin mulkin Amurka, wanda gaba ɗaya bai yi daidai da Najeriya ba

Ikeja, jihar Legas - Tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa, Cif Bode George, ya ce al’amura ba sa tafiya daidai a Najeriya ne, saboda kwafo tsarin mulkin ƙasar daga kundin tsarin mulkin ƙasar Amurka.

George ya bayyana hakan ne a yayin da yake gabatar da jawabi a matsayin babban bako a wajen wata lakca da 'SWAAYA Limited', mawallafan kafar labarai ta 'Freedom online' suka shirya kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Farashin Litar Man Fetur Ya Ƙara Tashi a Najeriya, Ya Haura N600 a Gidan Man NNPCL

An yi wa lakcar take da “2023-2027: ’Yan Najeriya, Zaɓaɓɓun shugabanni da abubuwan da ake fata daga garesu."

Bode George ya ce dole ne a sake fasalin kundin tsarin mulkin Najeriya
Bode George ya nemi a sake duba kundin tsarin mulkin Najeriya saboda kwaikwayon Amurka da aka yi. Hoto: @abati1990
Asali: Twitter

Akwai buƙatar sake duba kundin tsarin mulkin Najeriya

Da yake jawabi a yayin taron wanda ya gudana a Otal ɗin Sheraton da ke Ikeja, jihar Legas, George ya ce kundin tsarin mulkin Najeriya ya yi tsauri sosai, saboda haka akwai buƙatar a sake duba shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jigon na PDP ya ce a matsayinsa na wanda ya yi aiki a gidan soja, ya fahimci cewa kundin tsarin mulkin Najeriya an gina shi ne bisa tsari na sojoji.

George ya bayyana cewa a tsari irin na gidan soja, umarni na zuwa ne daga na sama zuwa na ƙasa, saɓanin tsarin dimokuraɗiyya, inda yake zuwa daga mutane zuwa shugabanni.

Tsarin da ake kai ba zai kai Najeriya matakin da ake fata ba - George ya ƙara bayani

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Farmaki Har Cikin Fada, Sun Halaka Babban Sarki a Najeriya

Jigon na PDP ya jaddada cewa kwafar kundin tsarin mulkin Amurka da Najeriya ta yi ne ya sa abubuwa ke ƙara komawa baya.

Ya ƙara da cewa yaudarar kai ne 'yan Najeriya su riƙa tunanin cewa wannan tsarin da ake kai zai kai ƙasar zuwa matakin da ta daɗe tana fata.

A rahoton New Telegraph, Bode George ya ce tsarin da ake kai a yanzu bai yi ba kwata-kwata, don haka akwai buƙatar a sake duba shi.

Jigon na PDP ya kuma nuna goyon bayansa ga batun samar da 'yan sanda na jihohi, yana mai bayyana cewa hakan zai tabbatar da samar da tsaro a ƙasa baki ɗaya.

Wani shaida na jam'iyyar PDP ya ba ta kunya a gaban kotu

Legit.ng ta kawo muku rahoton wani shaida da jam'iyyar PDP ta gabatar a gaban kotun sauraron ƙararrakin zaɓen jihar Ogun.

Kara karanta wannan

Tsagerun 'Yan Bindiga Sun Buɗe Wa Mutane Wuta a Gargruwa 2, Sun Halaka Mutane da Yawa

Shaidan ya yi baki biyu bayan iƙirarin farko da ya yi na cewa shi wakilin PDP ne na akwatu a yayin zaɓen gwamna da ya wakana a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng