Abubakar Kyari: Abubuwa 10 da Aka Jahilta Tattare da Sabon Shugaban Jam’iyyar APC

Abubakar Kyari: Abubuwa 10 da Aka Jahilta Tattare da Sabon Shugaban Jam’iyyar APC

  • Yanzu ba sabon labari ba na cewa Abdullahi Adamu ya sauka daga kan kujerar shugaban APC
  • Tsohon Sanatan Nasarawan ya ba Sanata Abubakar Kyari wuri ya jagoranci majalisar NWC
  • Sakataren APC na kasa ya ajiye kujerarsa, Festus Fuanter ya samu mukamin rikon kwarya

Abuja - A rahoton nan, Legit.ng Hausa ta tattaro bayanai game da Sanata Abubakar Kyari wanda ragamar jam’iyyar APC ta fada a hannunsa a yau.

1. Haihuwar Abubakar Kyari

A jihar Kaduna aka haifi Abubakar Kyari CON a ranar 15 ga Junairun 1963, a lokacin mahaifinsa ya na Gwamnan sojan tsohuwar jihar Arewa ta tsakiya.

Mahaifin na sa, Birgediya Janar Abba Kyari ya haifi wasu yara tara kafin ya rasu. Bayanan shafinsa sun nuna shi kuwa ya na da 'ya 'ya hudu da matarsa.

Kara karanta wannan

APC Ta Tabbatar da Cewa Shugaba da Sakataren Jam'iyya Sun Yi Murabus, Ta Maye Gurbinsu

2. Fara makarantar boko a gida

A 1974 Abubakar Kyari ya shiga makarantar Kaduna Capital School, bayan nan ya zarce Barewa College da ke garin Zariya, ya samu shaidar WASSCE.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jam’iyyar APC
Sabon Shugaban Jam’iyyar APC, Abubakar Kyari Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

3. Kyari ya yi jami’a a kasar Amurka

Kyari ya kammala digirin farko a jami’ar Tennessee Martin a Amurka a 1986, bayan shekaru uku ya samu digirgir na MBA daga jami’ar St.Louis Missouri.

4. Fara rike kujerar siyasa

Bayan da aka samu a shafin APC ya nuna a 1998, Kyari yana cikin wadanda su ka zama ‘yan majalisar wakilai, ya lashe zabe a karkashin jam’iyyar UNCP.

5. Shirin zaben 1999

Bayan kujerar majalisar tarayya, ‘dan siyasar ya zama ma’ajin jam’iyyar APP na reshen jihar Borno, ya rike matsayin nan ne kafin a shirya zabe a 1999.

6. Komawa majalisar tarayya

A 1999 Kyari ya koma majalisa a Abuja yana shekara 36 a Duniya. ‘Dan majalisar na Borno yana cikin ‘yan jam’iyyar hamayya a mulkin Olusegun Obasanjo.

Kara karanta wannan

Muhimman Abubuwa 5 Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Sabon Shugaban Riko Na Jam'iyyar APC

7. Kwamishina a jihar Borno

Daga 2003 zuwa 2011, sabon shugaban rikon kwaryan na APC ya zama Kwamishina a Borno sau biyar. Na farko kwamishinan ruwa daga 2003 zuwa 2005.

Daga baya ya yi shekaru shida a jere a matsayin Kwamishinan ayyuka, na harkokin ruwa da na harkokin gida da yada labarai a gwamnatocin ANPP.

Bayan haka, jagoran na APC ya kasance shugaban hukumar kula da ruwan sha na jihar Borno.

8. Kyari a fadar Kashim Shettima

Daga kwamishinan ayyuka, Gwamna Kashim Shettima (a lokacin) ya dauko Kyari ya nada shi a shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin Borno a Maiduguri.

9. Majalisar Dattawa sau biyu

Daga fadar gwamna Kyari ya nemi takarar Sanatan Borno ta Arewa a majalisar dattawa, a karshe kuwa ya yi nasara aka rantsar da shi a Yunin 2015.

A zaben 2019 da ya sake yin takara, Sanatan ya doke abokan gabansa, daga nan ne tsohon mai gidansa watau Kashim Shettima ya zama abokin aikinsa.

Kara karanta wannan

Kura-Kurai, Katobara da Cikas 7 da Abdullahi Adamu Ya Samu a Kujerar Shugabancin APC

10. Shugabancin jam’iyyar APC

Da aka warewa Arewa maso gabas kujerar mataimakin shugaba a APC, Kyari ya yi nasara a 2022. Wannan ya jawo ya hakura da kujerarsa a majalisa.

Abdullahi Adamu ya tafi

Rikicin APC ya dauki salo na dabam yayin da Abdullahi Adamu ya rubuta takardar murabus, rahoto ya zo cewa Sanata Adamu ya ajiye mukaminsa.

Abdullahi Adamu ya bi sahun Mai Mala Buni, Adams Oshiomhole da John Oyegun a Jam’iyya mai-ci, kusan dukkansu ba a yi rabuwar jin dadi da su ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng