APC Ta Tabbatar da Adamu da Omisore Sun Yi Murabus Daga Mukamansu

APC Ta Tabbatar da Adamu da Omisore Sun Yi Murabus Daga Mukamansu

  • Shugaban jam'iyyar APC ta ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu da sakataren jam'iya, Iyiola Omisore, sun sauka daga muƙamansu
  • Kwamitin gudanarwar APC (NWC) ne ya tabbatar da murabus ɗin Adamu da Omisore ranar Litinin, 17 ga watan Yuli, 2023
  • Bayan tsawon lokaci ana yaɗa jita-jita, NWC ya tabbatar da murabus ɗin jiga-jigan biyu a taron da ya gudana karkashin jagorancin Abubakar Kyari

FCT Abuja - Kwamitin gudanarwan jam'iyyar APC ta ƙasa (NWC), a ranar Alhamis, 17 ga watan Yuli, ya tabbatar da cewa shugaban jam'iyya, Abdullahi Adamu ya yi murabus.

Mukaddashin shugaban APC, Sanata Abubakar Kyari ne ya tabbatar da lamarin yayin zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan kammala taron NWC a Abuja.

Hoton Omisore da Adamu.
APC Ta Tabbatar da Adamu da Omisore Sun Yi Murabus Daga Mukamansu Hoto: OfficialAPCNg
Asali: Twitter

Bugu da ƙari, ya ce sakataren APC, Sanata Iyiola Omisore, ya bi sahun Adamu, shi ma ya yi murabus daga kujerarsa, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito

Kara karanta wannan

Karin Bayani: An Samu Babbar Matsala a Wurin Taron APC Na Ƙasa, Sakatare Ya Fice Daga Wurin

Sanata Kyari ya karbi ragamar APC, ya tabbatar da murabus din Adamu da Omisore

Mista Kyari ya ƙara da bayanin cewa tuni ya maye gurbin Adamu a matsayin muƙaddashin shugaban APC yayin da mataimakin sakatare, Barista Festus Fuanta ya koma muƙadɗashin Sakatare na ƙasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka zalika ya sanar da ɗage taron masu ruwa da tsakin APC da taron majalisar zartarwa (NEC) daga ranakun Talata da Laraba har sai baba ta gani.

Waɗanda suka halarci taron gaggawa a sakatariyar APC da ke Abuja

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa mambobin kwamitin gudanarwa NWC 17 duk sun samu halartar taron na gaggawa yau Litinin a babbar sakatariyar APC ta ƙasa.

Sai dai mutum biyu, wanda suka kunshi sakataren watsa labarai, Felix Morka da shugabar mata, Betta Edu, ne kaɗai ba su halarci taron ba bayan sun bada uzuri.

Kara karanta wannan

Kura-Kurai, Katobara da Cikas 7 da Abdullahi Adamu Ya Samu a Kujerar Shugabancin APC

Rikici a Sakatariyar APC Yayin da Sakatare Na Ƙasa Ya Fice Daga Wurin Taro a Abuja

A ɗazu mun kawo muku cewa Sanata Iyiola Omisore ya bar babbar sakatariyar APC da ke birnin tarayya Abuja ba tare da ya tsaya ya saurari manema labarai ba.

Sakataren APC ya bar wurin taron NWC na gaggawa bayan hana shi shiga, a cewarsa ya zo wurin Abdullahi Adamu ne amma bai gansa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262